Xan takara yayiwa mutum sama da 7000 aikin kiwon lafya kyauta a Nasarawa Daga Zubairu T M Lawal Lafia Doktan Talakawa kuma xan takarar kujerar Majalisar wakilai na Tarayya mai wakiltar mazaver Lafia da Obi Hon Joseph Haruna Kigbu yayiwa dubban alumman masamman talakawa dake halin kunci aikin kiwon lafiya kyauta. Duk da cewa wanan aikin ba shine farauba da jama’a suka saba gani wajen Dakta Joseph Haruna Kigbu. Wanda ya kwashe sama da shekara goma sha hudu yana gabatar da wanan aikin na taimakawa talakawa. Hakan nema yasanya alumma keyimasa laqabi da suna (Daktan Talakawa). A kwanakin baya Daktan talakawan ya gudanar da makamanciyar irin wanan aiki na kiwon lafiya a cikin garin Lafia inda aka gudanar dashi a kofar gidan Sarkin Lafia sama da mutum dubu hudu suka amfana da wanan shirin. Sai dai a wanan lokacin an gudanar da shirin kiwon lafiyar a gurare biyu ne. Garin Dodoguru inda ake saran kimanin mutum dubu uku zasu amfana da wanan tallafin na Daktan Talakawa. Sai garin Adogi inda sama da mutum dubu zasu amfana da wanan shirin. Sama da Likitochi 60 ne suke gudanar da wanan aikin a garuruwa biyun. Shirin da zai kwashe yini hudu ana gudanar dashi ya samu halartan kwararon Likitochi dsga fannoni dabam dabam. Kuma komai kyatane tun daga kati zuwa magunguna. Za’a gudanar da Fida ga duk wanda yake da lalurar Fida tare da aikin IDO da Qaba cutarn Hanta da Tb da kuma kunni da sauransu. Kamar masu cutar Daji da bazai yuhu ayi masu aiki a nan gurarenba za’a basu takarda da zasuje manyan Asibitochi kamar ta Jos ko ABU Zaria ko Abuja ko Keffi inda a nan za’a yi masu aikin Fida batare da biyan koda kandala ba. Da yake jawabi ga tawagar Daktan Talakawa Sarkin Dodoguru Mista .Jonathan Iwala yace; duk da cewa wanan aikin da Daktan Talakawa Hon. Joseph Haruna Kigbu yakeyi ba Sabon abubane gurin alumman jihar Nasarawa amma a yau abin farin cikine tunda har cikin gari na akazo . Sarkin yayi roko ga alumman yankin Dodoguru dasu zamo masu bin komai bisa tsari da kwanciyar hankali. Sannan yayi kira ga alumman dasu zamo masuyiwa Daktan Talakawa adu’a saboda irin wannan gudumawar da yake badawa na kiwon lafiya shine abinda kowa ke buri . Dayake jawabi ga manema Labarai Daktan Talakawa Hon.Joseph Haruna Kigbu yayi godiya da Allah yabashi ikon taimakawa talakawa ta wannan vangaren. Yace; iyayansa Talakawa ne kuma sun sha wahala wajen biya masa kudin Makaranta yayi karatu saboda haka shima burinsa yaga ya taimakawa talakawa a dukkan lokaci bashi da wani buri kamar yaga Talakawa suna walwala suna jin dadi a rayuwa. Daktan Talakawa yace; koda siyasa ko babu siyasa fatanmu mu taimakawa talakawa masamman a vangaren kiwon lafiya . Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu ta hanyar godiya da irin wannan tallafin kiwon lafiyan da Daktan Talakawa yake masu. Dubban alumman maza da matane dai suka halarci dukkan guraren da ake gudanar da tallafin kiwon lafiyan.

Xan takara yayiwa mutum sama da 7000 aikin kiwon lafya kyauta a Nasarawa Daga Zubairu T M Lawal Lafia Doktan Talakawa kuma xan takarar kujerar…

View More Xan takara yayiwa mutum sama da 7000 aikin kiwon lafya kyauta a Nasarawa Daga Zubairu T M Lawal Lafia Doktan Talakawa kuma xan takarar kujerar Majalisar wakilai na Tarayya mai wakiltar mazaver Lafia da Obi Hon Joseph Haruna Kigbu yayiwa dubban alumman masamman talakawa dake halin kunci aikin kiwon lafiya kyauta. Duk da cewa wanan aikin ba shine farauba da jama’a suka saba gani wajen Dakta Joseph Haruna Kigbu. Wanda ya kwashe sama da shekara goma sha hudu yana gabatar da wanan aikin na taimakawa talakawa. Hakan nema yasanya alumma keyimasa laqabi da suna (Daktan Talakawa). A kwanakin baya Daktan talakawan ya gudanar da makamanciyar irin wanan aiki na kiwon lafiya a cikin garin Lafia inda aka gudanar dashi a kofar gidan Sarkin Lafia sama da mutum dubu hudu suka amfana da wanan shirin. Sai dai a wanan lokacin an gudanar da shirin kiwon lafiyar a gurare biyu ne. Garin Dodoguru inda ake saran kimanin mutum dubu uku zasu amfana da wanan tallafin na Daktan Talakawa. Sai garin Adogi inda sama da mutum dubu zasu amfana da wanan shirin. Sama da Likitochi 60 ne suke gudanar da wanan aikin a garuruwa biyun. Shirin da zai kwashe yini hudu ana gudanar dashi ya samu halartan kwararon Likitochi dsga fannoni dabam dabam. Kuma komai kyatane tun daga kati zuwa magunguna. Za’a gudanar da Fida ga duk wanda yake da lalurar Fida tare da aikin IDO da Qaba cutarn Hanta da Tb da kuma kunni da sauransu. Kamar masu cutar Daji da bazai yuhu ayi masu aiki a nan gurarenba za’a basu takarda da zasuje manyan Asibitochi kamar ta Jos ko ABU Zaria ko Abuja ko Keffi inda a nan za’a yi masu aikin Fida batare da biyan koda kandala ba. Da yake jawabi ga tawagar Daktan Talakawa Sarkin Dodoguru Mista .Jonathan Iwala yace; duk da cewa wanan aikin da Daktan Talakawa Hon. Joseph Haruna Kigbu yakeyi ba Sabon abubane gurin alumman jihar Nasarawa amma a yau abin farin cikine tunda har cikin gari na akazo . Sarkin yayi roko ga alumman yankin Dodoguru dasu zamo masu bin komai bisa tsari da kwanciyar hankali. Sannan yayi kira ga alumman dasu zamo masuyiwa Daktan Talakawa adu’a saboda irin wannan gudumawar da yake badawa na kiwon lafiya shine abinda kowa ke buri . Dayake jawabi ga manema Labarai Daktan Talakawa Hon.Joseph Haruna Kigbu yayi godiya da Allah yabashi ikon taimakawa talakawa ta wannan vangaren. Yace; iyayansa Talakawa ne kuma sun sha wahala wajen biya masa kudin Makaranta yayi karatu saboda haka shima burinsa yaga ya taimakawa talakawa a dukkan lokaci bashi da wani buri kamar yaga Talakawa suna walwala suna jin dadi a rayuwa. Daktan Talakawa yace; koda siyasa ko babu siyasa fatanmu mu taimakawa talakawa masamman a vangaren kiwon lafiya . Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu ta hanyar godiya da irin wannan tallafin kiwon lafiyan da Daktan Talakawa yake masu. Dubban alumman maza da matane dai suka halarci dukkan guraren da ake gudanar da tallafin kiwon lafiyan.