Ra’ayin Malaman Izala ya rabu Atiku zamu zabe ba Buhari ba

Ra’ayin Malaman Izala ya rabu Atiku zamu zabe ba Buhari ba

– Sheikh Sambo Rigachikun

Daga Madina Ibrahim

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya kuma jigo a kungiyar Izala, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya ce dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar zai zaba a zaben 2019.

A karshen makon jiya ne kungiyar Izala a kasar, ta bukaci mabiyanta da su zabi Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, wanda yake neman wa’adi na biyu.

A tattaunawar da wakilinmu BBC Mustapha Kaita ya yi da Shiekh Sambo, ya bayyana dalilan da ya sa yake goyon bayan Atiku Abubakar.

“Zai zabi mutumin da ya fi taimakon addinin Musulunci da taimakon jama’a da kuma amfanar da mutanen kasa,” in ji shi. Yace ;

Mu ba mu karbi kudin makamai ba – Kungiyar Izala
Malamin dai ya bayyana karara cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne zabinsa a 2019

Har ila yau, malamin ya yi ikirarin cewa ya kwashe shekara 30 yana tare da Atiku, inda ya ce dan takarar ya “gina masallatan Juma’a fiye da 100.”

Ana dai ci gaba da samun rabuwar kai a bangaren malaman Izala a Najeriya.

A ranar Asabar ne Kungiyar Izala daya daga cikin manyan kungiyoyin addinin Islama a Najeriya ta ce Shugaba Buhari take goyon baya a zaben 2019.

Shugaban kungiyar na kasa Shiekh Abdullahi Bala Lau ya ce sun yanke shawarar ne bayan wani taro na kasa da suka gudanar.

Ya ce sun lura yadda ake fuskantar lokacin zabe mawuyaci, “ya kamata a yi saitin al’ummar Musulmi kan abin da ya kamata.”

“Allah ya kawo saukin rigingimu da tashin bama-bamai dalilin zuwan Shugaba Buhari, illa dan abin da ya rage na fitintinun, Allah zai kawo saukinsu,” in ji Sheikh Bala Lau.

4 Replies to “Ra’ayin Malaman Izala ya rabu Atiku zamu zabe ba Buhari ba”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *