BABBAN MAGANA ; Za a maida Saudiyya wani yankin nishadantarwa na Duniya

BABBAN MAGANA ; Za a maida Saudiyya  wani yankin nishadantarwa na Duniya

Daga Aliyu Mustapha

Saudiyya ta bayyana shirye-shiryen da ta ke yi na bunkasa bangaren nishadi a kasar, wanda ya hada da bai wa gidajen abinci takardar izinin gudanar da nishadi kai tsaye, kamar yadda ake yi a kasashen Turai.

Shirin da za a kaddamar a 2019 zai kunshi shigo da taurari kamar su Jay Z da David Beckham.

Saudiyyar ta bayyana shirye-shiryen ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kisan gillar dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

Kokarin da ake yi na mayar da Saudiyya wani yankin nishadantarwa na daya daga cikin abubuwan da Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman ke yi, wanda lamarin kisan Jamal khashogji ya mutukar bata wa suna.

Ko a watan Fabrairun 2018 ma Saudiyya ta ce za ta ware kudi dala biliyan 64 domin bunkasa masana’antunta na nishadantarwa a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban hukumar da ke kula da harakokn nishadi a kasar ya ce an tsara shirya abubuwa kimanin 5,000 a bana kawai, da suka kunshi har bikin cashewa na Maroon 5 kamar irin wanda ake gudanarwa a Amurka.

Akwai kuma bikin casu na Cirque du Soleil irin wanda ake gudanarwa a kasashen Turai.

Tuni dai Saudiyya ta fara aikin gina wajen casu a birnin Riyadh.

Shirin zuba jarin na cikin sabbin manufofin bunkasa tattalin arziki da ake kira Vision 2030 wanda Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya kaddamar shekaru kusan uku da suka gabata.

 

 

2 Replies to “BABBAN MAGANA ; Za a maida Saudiyya wani yankin nishadantarwa na Duniya”

  1. bai kamata ba kasar da’ake bautar Allah ace xa’abude wajen sa6o kuma karkumanta idan akace Amerika sun xauna A saudiyya Xasu yake muslunci ne shiyasa sufito ta hakan sbd sunga batayan xasu fito ne shiyasa yakamata Adakatar da wannan shirin Da’ake shiri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *