MUTUWA TONO ASIRI ; An kore iyalan Marigayi Sarkin Lafia kan rashin biyan kudin makaranta.

An kore iyalan Marigayi Sarkin Lafia kan rashin biyan kudin makaranta.

Daga  Zubairu T M Lawal Lafia

Kasa da wata daya da Mutuwar Sarkin Lafia Dakta Isa Mustapha Agwai wasu dalubai cikin iyalansa  sun fara fuskantar matsala a karantunsu.

Kimanin yara 27 cikin 58 dake karatu a wasu Makarantu dabam dabam dake qasan nan aka kora sakamakon rashin kudin makaranta.

Marigayi Sarkin Lafia Dakta Isa Mustapha Agwai yana daukar nauyin dalubanne yana biya masu kudin Makaranta, da sauran hidin dimunsu.

Duk da cewa ba ya’yansane na cikinsa ba amma ya’yan yan Uwa da abokan arziki wadanda ya rike tankar ya’yan da ya Haifa a cikinsa.

Bayan mutuwar Sarkin da mako daya ne wasu suka koma makarantunsu domin cigaban karatu na zago na biyu.
Akasarin wadanan dalubai 58 suna rayuwani karkashin kulawar Marigayi Isa Mustapha Agwai. A yanzu haka rayuwarsa tana fama da tangarda na rashi mai daukar nauyin karatunsu .

Akwai kimanin yara 21 da ake ganin suma zasu fuskanci irin wanan matsalar matukar kungiyar Malaman jami’a suka jenye yajin aiki.

Akwai yara dake karatu a jami’o’i na gida da waje da suka hada da Jami’ar qasar Sudan da Niger da Saudi Arabia da sauransu. Wadanda Marigayin shine yake daukar nauyin karatunsu.

Ana kaytata zaton zasu samu matsala ta vangaren karatunsu sakamakon sun rasa uba dake daukar nauyin karatunsu.
Haka zalika akwai kimanin gidajen da dama dake Anguwar Kaura da sauran su da Marigayin ke kulawa da cinsu da shasu, yanzu haka wasunsu rayuwarsu ya fara fiskantar matsala.

Sanan akwai yara qanana dake karatu a Nusiri da Firamare da Sakondire da marigayi sarki Mustapha Agwai ke daukar nauyin biyan kudin makarantunsu suma idan ba ayi sa’a ba zasu fuskanci matsalar rayuwa.

Daya daga cikin yaran da Marigayin yake daukar nauyin karatunsu kuma shi dalubine da ya kamala karatunsa a Key Science Academy Masaka ya kuma zarce zuwa Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake garin Lafia.

Ya shedama wakilinmu irin tsananin da ya shiga saboda mutuwar Marigayin .

Sakamakon shiya dauki dawainiyar karatunsa yake taimakawa rayuwarsa ya daukeshi tankar yaron cikinsa . idan ba’a samu wanda zai taimaka masu ba to lalai karatunsu zai katse a hanya.

Sai dai a tabakin Sakataren fadar  Malam Hudu mai Lafiya yace: yanzu dole a shiga matsasi sakamakon halin da ake ciki na rashin wanda zai maye gurbin Marigayin. Hakan ya sanya komai suka tsaya cif , na harkokin yau da kullun a fadar.

2 Replies to “MUTUWA TONO ASIRI ; An kore iyalan Marigayi Sarkin Lafia kan rashin biyan kudin makaranta.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *