An samu nasarar inganta alurar riga kafin a jihar Barno Inji Dr. Sule Mele

An samu nasarar inganta alurar riga kafin a jihar Barno

Inji Dr. Sule Mele

Daga Zubairu M.Lawal

Babban jami’in kula da harkan Lafiya ta jihar Barno Dakta Sule Mele ya nuna farin cikinsa da yadda aka samu nasarar aiwatar da alurar riga kafin cutar shan inna a jihar Barno ga yara kanana wadanda shekarunsu yakai matakin gudanar da alurar.

A kwanakin bayane dai hukumar kuma da harkokin kiwon lafiya ta Majalisar [inkin Duniya ta kara karfi wajen ganin an gudanar da harkan kiwon lafiya a jihohin dake Arewa maso gabas.

Dakta Sule Mele yace;alurar rigakafin cutar shan inna ya samu dammar gudana a kauyuka da unguwanni dama sansanonin yan gudun hijira dake jihar Barno.

Ya kara da cewa, dammar da muka samu nayin amfani da Shugabannin alumma dana kungiyoyin karkara yayi tasiri wajen wayar dakan alumma masamman iyaye da suka bada gudumawa wajen kawo yaransu.

Hukumar kula da kiwon lafiya ta Majalisar [inkin Duniya wato (WHO) ta samu gudumawar wasu kungiyoyi da suke da fatan samar da wadacecen ganin an samu zaman lafiya a wanan yankin ta Arewa maso gabas. suma kungiyoyin sun taka rawa wajen wayar dakan iyaye saboda su rika mika y’yansu ana masu alurar.

Hukumar bada agaji tabangaren kula da kiwon lafiya ta samar da ingantatun magunguna da sinadari masu gina jiki ga lafiyar yara }anana.

Dakta Sule Mele yace; alumman }ar}ara da lungu sako sum amfana da wannan tallafin na kiwon lafiya kuma zai magance barazanar cutar maleriya dake addabar alumman }ar}ara dama mazauna guraren dake kusa da ruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *