BABBAN MAGANA – INEC bazataba wani Gwamnan da YAN majalisu takardan shedar lashe zabe ba

BABBAN MAGANA – INEC bazataba wani Gwamnan da YAN majalisu takardan shedar lashe zabe ba

Aliyu Mustapha

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da bada takardan shedar lashe zabe ga yan takarar Gwamnan a jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

Tare da yan Majalisar dokokin jihar guda 24. A yau Laraba kamar yadda ta sheda zata mikawa Gwamnoni da yan Majalisun da sukayi nasara takardan shedar lashe zaben.
Hukumar zabe tabi Umurnin wata Babban kotu dake Sokoto da ta sauke zaben fidda gwani da bangaren , Gwamna Abdul’aziz Yari sukace anyi .

Rikicin zabe a jihar Zamfara dai ba sabon abu bane wanda yakici yaki cinyewa tun a lokacin zaben fidda gwani , ya’yan jam’iyyar APC suke ta kai ruwa rana , ta yadda har suka gagara gudanar da zaben fidda gwani na Gwamnan jihar da yan Majalisa .

2 Replies to “BABBAN MAGANA – INEC bazataba wani Gwamnan da YAN majalisu takardan shedar lashe zabe ba”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *