Mahara sunyi garkuwa da matar Shugaban yan jarida a Nasarawa

Mahara sun budewa Motar yan jarida wuta a Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal

Wasu mahara da ba atantace kosuwaye ba sunyi Garkuwa da Matar Shugaban YAN Jarida bangare manema labarai na jihar Nasarawa.

Lamarin ya farune da misalin karfe 7pm na yammacin yau Laraba . Da yake zantawa da manema labarai Alhaji Sulaiman Abubakar Lawal yace; sun taho suna zuwa dai dai garin Gudi dake yankin karamar Hukumar Akwanga.
Yace ; maharar sun harbi motar suka fasa tayan motar dole ta tsaya . maharar sun tafi da matar Shugaban YAN jaridar tare da wasu matan da suke cikin motar bayan sun baro cibiyar Bautar kasa dake garin Keffi (NYSC).
Yace; bayan sun harbi motar sai da ta juya ta data mangari wani guri ta tsaya .
Cikin matan da aka tafi dasu Malam Yahanasu Abubakar Matar Sulaiman Abubakar Lawal wakilin Radion Nagarta, a jihar Nasarawa. Da matar tsohon Dan Majalisar dokoki na jihar Nasarawa mai wakiltar mazaber Obi 1 . Alhaji Sidi Bako da sauransu.

Tuni Rundunar yan Sanda ta bakin jami’in hulda da Jama’a ASP Sama’ila Usman yace, sun dauki matakin dakile wanan aikin ta’addanci .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *