PDP da APC zasu kai ruwa rana a majalisar Najeriya

PDP da APC zasu kai ruwa rana a majalisar Najeriya

 

Daga Madina Ibrahim

Cacar baki ta barke tsakanin jam’iyyar PDP mai adawa da APC mai mulki, bayan APC ta ba ‘ya’yanta umarnin su mamaye dukan mukaman majalisar dokokin kasar da ke Abuja, kasancewarsu su ne masu rinjaye.

Sai dai jam’iyyar PDP ta kalubanci wannan umarnin, inda ta bukaci ‘ya’yanta da su yi takarar kowane mukami da ke majalisar.

A shekarar 2015, jam’iyyar PDP ta shammaci APC inda danta ya samu kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Kuma mukaman shugaban majalisar dattawa da kuma na wakilai suka shiga hannayen da jam’iyyar ta ce ba su kwanta mata ba.

PDP ta ce babu wata doka da ta hana ‘ya’yanta neman shugabancin majalisun kasar biyu da na muhimman kwamitoci.

Sakateren jam’iyyar PDP Sanata Ummaru Tsauri ya ce tsarin mulkin Najeriya bai ce “dole sai wane, ko wane ba.”

Sai dai Sakataren Walwalar jam’iyyar APC Alhaji Ibrahim Masari ya ce har yanzu suna kan bakarsu.

“Wanda duk yake da rinjaye shi ne zai zama shugaban majalisar dattawa da kuma na wakalai,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *