Sabon Rikicin kabilanci: ya barke a jihar Nasarawa

Sabon Rikicin kabilanci: ya barke a jihar Nasarawa

Aliyu Mustapha

An kashe mutane biyu tare da kone gidaje 38 a wani rikicin kabilanci da ya barke a garin Andaha da ke karkashin hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Mazauna kauyuka uku da ke kusa da garin da rikicin ya faru sun kaurace wa gidajen su saboda tsoron kai harin daukan fansa a kan su.

Mutanen sun fara kauracewa gidajen su ne bayan samun rahoton kashe wata budurwa mai shekaru 19 da ake zargin wasu makiyaya da aikata wa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa, Samaila Usman, ya tabbatar da afkuwar rikicin ga gidan Talabijin na Channels a hirar su da shi ta wayar tarho.

A cewar sa, rikicin ya samo asali ne bayan wasu da ake zargin makiyaya ne sun yiwa wasu mata uku ‘yan kabilar Mada fyade yayin da suke dawowa daga wurin wani biki da suka halarta a garin Katanza.

Kakakin ya bayyana cewar makiyayan sun lakada wa Joy Danlami; daya daga ‘yan matan da suka yiwa fyade, duka, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ta.

” Wasu makiyaya sun kai wa wasu ‘yan matan kabilar Mada hari a hanyar su ta dawowa daga wurin biki, sun yiwa wata mai suna Joy Danlami fyade sannan nan sun lakada ma ta duka.

“Y’an uwanta sun dauke ta zuwa babban asibitin garin Akwanga inda daga bisani ta mutu. Hakan ne yasa matasan kabilar Mada suka hada kan su tare da kai hari sansanin makiyaya inda suka kashe mutum daya sannan suka kone wurin.

“Daga baya su ma makiyayan sun hada kai tare da kai harin daukan fansa a kauyukan Nidam da Maite, inda suka kone gidaje masu yawa,” a cewar Usman.

Kafin afkuwar wannan rikici, jama’ar garuruwan Nidam, Maite da Katanza na zaune cikin lumana da juna na tsawon shekaru masu yawa.

Wasu mazauna yankin da suka tattauna da majiyar mu, sun yi kira ga gwamnati da ta kawo masu dauki domin kare afkuwar wani rikicin a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *