Majalisar [inkin Duniya da kasar japan sun inganta rayuwar yan gudun hijirar Barno

Majalisar [inkin Duniya da kasar japan sun inganta rayuwar yan gudun hijirar Barno

Daga Zubairu .M. lawal

Majalisar [inkin Duniya da }asara Japan sun hada giwa wajen inganta rayuwar yan gudun hijira da marasa galihu a Duniya. A wani shirin koyar da harkan nomar shinkafa ta masamman da yadda ake tsaftace shinkafa yazama mai inganci mar tsakuwa da duwatsu. An koyar da mata dake zaune a sansanin yan gudun hijira dake yankin Maiduguri dake Arewa maso gabashin Nijeriya.

Shirinda aka gabatar a sansanin yangudun hijira dake garain El-Miskin ya koyar da mata sama da 300 yadda zasu rika sarafa shinkafa ya koma tsaftacece tankar ta }as ashen waje.

Cikin wadanda suka samu kwarewa a wanan koyarwan wata mai suna Binta Bani wanda take da yara goma “ tace na kwashe sama da shekaru hudu ina zaune a wanan sansanin sakamokon yadda rikicin Boko Haram ya lalata garinmu muke zaune a nan.” Ta }ara da cewa nayi nasara saboda wanan koyarwan da akayimana ya taimakeni koda zanyi noman shinkafa na san yadda zan kula da tsaftaceshi.

Itama Rebecca Ibrahim mai shekara 35 tana zaune da ya’ya biyu a wanan sansanin “ tace na baro garin Gwazane saboda yadda rikicin Boko Harama ya lalata garinmu aka kasha yan uwa na” tace wanan koyarwan ya taimakamini zan kuma kula da yinsa koda sana’ar aikataune domin samun abinda zain ci tare da wadannan }ananan yara.

}asar Japan ta dauki wanan shirin ne saboda taimakawa Mata da suke cikin irin wanan hali da kuma mazaje masu rauni. Hakan yasanya ta samu kwarin Giwar tafiyar da wanan shirin tunda ta hada hannu da Majalisar [inkin Duniya

Da take Magana a madadin Hukumar kula da bada abinci ta Duniya dake bangaren Majalisar [inkin Duniya Misis Lilian Ngusuur ,tace a kalla samada mutum miliyon biyu da rabi suka amfana da wanan shirin na koyan tsaftace abinci.

Tace shinkafa yana cikin tsarin abinchi ta Duniya da yanzu akafi amfani dashi, kuma Majalisar [inkin Duniya tana taimakawa yan gudun hijira da sana’o’I da zasu dogara da kawunansu. Wanan sana’a zai taimaka masu tsawan rayuwansu da yaransu. Wanan shirin na nomad a tsaftace shinkafa bay a tsayane ga manyan mata kawao ba harma da }anana dama Mazaje.

Ta }ara da cewa wanan shirin ba zai tsaya a adadin mata 300 bane zai zarce hakan tunda yanzu an farane a Nijeriya amma a wasu }asashe tuni shirin yayi nisa. Haka zalika za’a fadada shirin zuwa Jihohin Yobe da sauran  sansanonin yan gudun hijira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *