BADAQALA- TSOHON GWAMNAN APC YA KASHE 2.3BILIYON A MAKABARTA

TSOHON GWAMNAN APC YA KASHE 2.3 BILIYON A MAKABARTA

Daga Zubairu Lawal

A jiya a wata ganawata da manema labarai a sakatariyar ýan jarida na ke bayyana musu cewar zargin da gwamnatin Bauchi take yi wa tsohowar gwamnatin jihar na kashe naira biliyan 2.3 don sayo likkafani da katakon bison mamaci yarfe ne kawai ake yadawa domin bata wa gwamnatin baya suna.

A cikin tattaunawar na tabbatarwa manema labaran cewar babu gaskiya kan adadin kudaden da ake yadawa da kuma bayanan da suka fito daga bakin mai magana da yawun Gwamna Dakta Ladan Salihu illa kawai soki burutsu da tsagwaron son zuciya.

A ýan kwanakin nan a sababbin Kafofin yada labarai na zamani da wasu jaridu an yi ta yada cewar tsohuwar gwamnatin jihar Bauchi a ƙarƙashin Gwamna M. A. Abubakar Esq ta sayo kayan biso na likkafani har na tsawon naira biliyan 2.3 a cikin wata biyar kacal.

Sam-sam wannan wata magana ce da hankali ma ba zai ɗauka ba sabo da tsagwaron ƙaryace marar tushe, domin kuwa adadin kudaden da ake yadawar ba haka ba ne, sannan tsawon lokacin da aka bayyana shima shaci faɗi ne kawai.

Don bayan ganin wannan labarin ke da wuya na garzaya domin na tuntubi tsohon kwamishinan hukumar kananan hukumomi Barr.

Nasirudin Muhammad kuma ya fayyace min komai dalla-dalla, ga kuma abin da ya ce min kamar haka: “Na karɓi shugabancin hukumar a watan Fabrairun na shekarar 2018 zuwa watan Mayun 2019 kuma duk wannan tsawon lokacin ba’a kashe rabin abin da sabuwar gwamnatin ke cewa an kashe ba. Abin da a ka kashe a tsawon wannan lokacin da na ke hukumar na kayan katakon biso likkafani bai wuce naira biliyan N1,270,743,520,”
Sabo da haka Kudaden da aka kashe biliyan 1.2 ne a tsawon zaman kwamishinan a hukumar da ke ɗaukar nauyin wannan aiki ba kamar yadda aka yada cewar biliyan 2.3 kuma a watanni biyar ba.

Har wa yau wani abun da aka boyewa jama’a shine, ba fa an kashe biliyan 1.2 ne a ƙaramar hukuma ɗaya ba kamar yadda a ke neman ɗora mutune a fahimtar hakan.

Tun bayan ɗarewar sabuwar gwamnati ba ta da wani aiki sai surutai da ƙoƙarin ɓatawa tsohon gwamnan jihar suna a idon duniya, don kawai shari’ar da ke yi mata barazana. A ganina bai dace ake yada karerayi don a yaudari jama’ar jihar ba.

Tunda tsohuwar gwamnatin ta bayar da kwangilar sayo kayan bison ta hanyar bin doka da oda da dukkanin ka’idodin bayar da kwangila kuma Kamfanonin da suka cika sharuda ne kuma na ýaýan jihar a ka bawa. Sannan an yi su a kan ƙa’ida to maye kuma na terere da batun? Sabo da haka Muna kira ga al’umman jihar Bauchi da su yi watsi da dukkanin wannan farfagandar da aka yada ko ake ci gaba da yadawa domin babu gaskiya a cikinsa ko kaɗan.

A na kokarin dauke hankalinsu ne don rashin kan gadon da gwamnatin ke ciki da rashin daukar hanyar magance matsalolin al’ummar jihar duk da dinbin biliyoyin kudaden da suka gada da kuma wadanda suka zo daga baya.

Idan za ku iya tunawa dai a wata hira da kakakin gwamnan jihar Bauchi, Dakta Ladan Salihu ya yi da manema labarai a kwanakin baya yake fadin cewar tsohowar gwamnatin ta kashe sama da biliyan biyu wajen sayo kayan binne mamaci. Wannan neman a yi ta yiwa sabuwar gwamnatin uziri ne bayan

da ta yi na nuna muhimman ayyuka a cikin kwana ɗarin farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *