Walwala zai ayi Tambuwal yayi kwamishinonin 28 da ma’aikatarsu

Jerin sunayen sabbin kwamishinonin Tambuwal 28 da ma’aikatarsu

Daga Ibrahim Lawal

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a ranar Alhamis 27 ga watan Yuni, 2019 ya raba ma’aikatu ga sabbin kwamishinoninsa su 28.
A wani zance da ya fito daga hannun Darakta Janar na yada labarai da al’amuran yau da kullum na gwamnan, Abubakar Shekara ya sanar cewa “daga cikin sabbin kwamishinonin akwai tsohon dan majalisar Sarkin Musulmi, Alhaji Isah Bajini Galadanci da kuma Abdussamad Dasuki, tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya.

Ga cikakken sunayen kwamishinonin da ma’aikatarsu
1. Hon Muhammad Arzika Tureta – Kwamishinan noma
2. Hon Usman Sulaiman Danmadamin-Isa – Kwamishinan cigaban karkara
3. Hon Abdussamad Dasuki – Kwamishinan kudi
4. Hon Abdulkadir Jeli Abubakar III – Kwamishinan harkokin cikin gida
5. Farfesa Aisha Madawaki Isah – Kwamishinan walwala da cigaban al’umma
6. Hon Abdullahi Maigwandu – Kwamishinan lamuran addini
7. Farfesa Abdulkadir Junaidu – Ma’aikatar lafiyar dabbobi da kifaye
8. Hon Bello Abukar Gwuiwa – Ma’aikatar ilimin firamare da sakandare
9. Dakta Shehu Kakale – Ma’aikatar kasafi da tsarin tattalin arziki
10. Hon Muhammad S. Arewa – Ma’aikatar al’adu
11. Bashir Gidado – Ma’aikatar cigaban cinikayya da kasuwanci
12. Sagir Attahiru Bafarawa – Ma’aikatar muhalli
13. Farfesa Bashir Garba – Ma’aikatar ilimin gaba da sakandare
14. Dakta Muhammad Ali Inname – Ma’aikatar lafiya
15. Hon Isah Bajini – Ma’aikatar yada labarai
16. Hon Sirajo Marafa Gatawa –Ma’aikatar filaye da gidaje
17. Dakta Kulu Haruna – Ma’aikatar kimiyya da fasaha
18. Col. Moyi Garba (rtd) – Ma’aikatar daukan aiki da tsaro
19. Hon Bello Bala Bodinga – Matasa da wasanni
20. Hon Kulu Sifawa – Mata da kananan yara
21. Hon Umar Bature – Ma’aikatar samar da ruwan sha
22. Hon Salihu Maidaji – Ayyuka
23. Hon Sani Bunu Yabo – Kaddamarwa da ayyuka na musamman
24. Hon Bello Aliyu Goronyo – Ma’adanan kasa
25. Hon Aliyu Balarabe Dandinmahe – Ma’aikatar man fetur
26. Hon Manir Muhammad Dan’iya, mataimakin gwamnan jihar shi ne zai kula da ma’aikatar kananan hukumomi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *