FATI WASHA TA SAMU BABBAN LAMBAN GIRMAMAWA A BIRNIN LONDON

FATI WASHA TA SAMU BABBAN LAMBAN GIRMAMAWA A BIRNIN LONDON

Daga Madina Ibrahim

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Fatima Abdullahi da ake kira Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka da aka gudanar a Birtaniya.

An sanar da Washa ne a matsayin gwarzuwar jaruma a taron karrama ‘yan Fim da aka gudanar ranar Asabar a birnin London.

Bikin wanda ake kira Afro Hollywood Awards ya shafi karrama jaruman fina-finan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka,

Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din ‘Sadauki.’
Jarumar ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a Fim din da ta fito “Jamila” da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a “Uwar Gulma”

Rahama Sadau ta wallafa hoton bidiyo a shafinta na Instagram, lokacin da Washa ta ke karbar kyautar, inda ta bayyana farin cikinta da godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *