KO KUNSA – ANA RIDISTAN MASU YIN FYADE A NIJERIYA

KO KUNSA – ANA RIDISTAN MASU YIN FYADE A NIJERIYA

Daga Musa Mahamud

Hukumar yaki da safarar mutane a Najeriya, Naptip, ta ce ta fara samu mutum 10 a cikin kundin rijistar masu aikata fyade da aka kaddamar.

A ranar Litinin ne aka kaddamar da sabon tsarin, wanda zai kasance wani kundi na dukkanin mutanen da aka samu da laifin cin zarafi ta hanyar lalata.

Rijistar za ta taimakawa hukumomin Najeriya hana wa wadanda aka samu da laifin cin zarafi ta hanyar lalata da suka hada da yin fyade tsallakawa zuwa sassan kasar domin sake aikata laifin.

Rijistar kuma ta kunshi sunayensu da lakabi da hotuna da shekaru da inda suke da kuma sauran bayanai wadanda mutane za su iya samu.

“Makasudin yin hakan shi ne don mutane su iya tantance wadanda za su yi hulda da su, misali idan za ka dauki malamin da zai koyar da yaranka, ko mai aikin gida, ko mai dafa abinci, ko direba ko duk wani ma’aikaci,” kamar yadda Ministar mata a Najeriyar Pauline Tallen, ta shaida wa BBC.
Ana fatan rijistar za ta hana wa masu aikata laifin samun guraben ayyuka a wasu wuraren.

Kididdigar da kungiyar kare hakkin mata ta Women At Risk International Foundation ta fitar, ya nuna ana cin zarafin dubban mata a kowacce rana a Najeriya.

Kaddamar da yin rijistar, wadda ita ce ta farko a kasar abin Allah-san barka ne kamar yadda kungiyoyin rajin kare hakkin mata suke gani.
Ya nuna yadda gwamnati ta zaburo don magance matsalar a fadin kasar.

Ministar mata Pauline Tallen, ta ce tuni aka yi wannan rijista a jihohi bakwai na kasar, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya ba su kwarin gwiwa da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifin yin fyade.

Sannan wannan hukunci zai fada kan hatta ‘yan siyasa ko ‘yan kasuwa ba zai gagari hukuma ba. Kan batun kare hakkin kananan yara ma ministar ta ce za ta yi rangadi a jihohin arewa kan hakan.

”Abin kunya ne a ce jihohin da ba su shiga rijistar kare hakkin yara mata ba na arewa ne, amma jihohin kudu duka sun yi.

Ba zan ambaci sunan jihohin ba, amma sun kai 10 a halin yanzu, zan je da kaina don rokar su shiga wannan rijista, saboda idan aka yi hakan sunan Najeriya zai shiga sahu mai kyau a Majalisar Dinkin Duniya.

Saboda duniya baki daya ta tashi haikan don magance matsalar fyade da cin zarafin mata,” in ji Pauline.

“Idan akwai rijistar, za a kaucewa daukar ma’aikaci mai aikata fyade da sauransu, kuma wadanda suke kauyuka da ba a kawo rahotonsu ba da zarar an samu an yi rijistar suyensu da sauran bayanai za mu dora daga inda muka tsaya,” in ji ta.

Batun cin zarafin mata da yi wa yara fyade na ci gaba da zama babban kalubale musamman a arewacin Najeriya, inda ake samun karuwar yi wa kananan yara mata fyade.
Wasu na ganin rashin gurfanar da wanda ake zargi da yin fyade gaban shari’a, da kokarin lullube batun da nufin rufa asirin wadda aka yi wa fyaden na kara ta’azzara matsalar, inda masu laifin ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *