Kofata a bude yake domin tattaunawa da yan jarida
Gwamnan Nasarawa
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana haka a lokacin bikin cin abinchi da karrama yan jarida da ya gudana a zauren taro na Ta’al dake garin Lafia.
Gwamnan ya yaba da kokarin da yan jarida keyi wajen nemo sashihan labarai da tantwncewa .yace; yan jaridar dake jihar Nasarawa mutanine dake aiki da hangen nisa.
Gwamnan yace; wanan karramawar da akayima wasunsu ya cancanta saboda duk cikansu suna aikin da ya kamata harma da kafafen yada labarai dake fadin jihar.
Ya qara da cewa “kofata a bude yake domin ganawa da kowani Xan jaridar da yake da abin cewa game da Gwamnati, dagani har Mataimakina bazamuyi kasa a giwa ba wajen baiwa yan jarida lokaci”.
Gwamnan yace ; game da ayyukan cigaba raya qasa nan bada dadewaba Gwamnati zata kawo babban Kamfanin aikin raya qasa ta kamfanin Dantata wadanda zasuyi aiki a wanan jihar.
Sanan mun kudduri aniyar samar da ilumin zamani na kirekire daga Makarantar Sakondire saboda yaranmu su tashi da fasaha da sana’a.
Mun dukufa wajen bunkasa harkan noma saboda muna da kasar noma da manomanmu zasu amfana. Sanan muna da albarkatun qasa da zamu bada mahimmanci agareshi domin samun aikinyi ga matasanmu .
Hukumar ilumin bai daya ta jihar Nasarawa taba da kwangilar gina ajujuwan karatu sannan zamu samar da kwararun Malami da zasu baiwa yara ilumi.
Muna kan bakarmu ta bunkasa tsaro domin samun dauwamamiyar zaman lafiya a ciki da wajen jihar.