MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA YABAWA BUHARI DA GWAMNATINSA

Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa Shugaba Buhari da Gwamnatinsa

Daga Zubairu M Lawal

Shugaban Majalisar wakilai ta Majalisar Dinkin Duniya a karni na 74 Farfesa Tajjani Muhammad Bande ya yabawa Shugaban qasar Nijeriya Alhaji Muhammad Buhari .

Shugaban Majalisar ta 74 Farfesa Tajjani Muhammad Bande yace; ayyukan cigaba da Gwamnatin Muhammad Buhari keyi.

Ya kara da cewa Gwamnatin ta samar da cigaba ga alumman Nijeriya  tare da yaki da miyagun yan Ta’adda dake addaban wasu yan kuna a kasar.

Ya qara da cewa Gwamnatin Nijeriya ta taka mahimmiyar rawa wajen ganin an samar da tsaro ga ma’aikatan agaji dama ofishin Majalisar Dinkin Duniya da yan Ta’adda suka taba kaima hari.

Yace; Majalisar Dinkin Duniya tana qara kawo agaji ga alumman Nijeriya da taimakawa marasa galihu yace; akwai shirye shirye da Majalisar Xinkin Duniya take yi wanda zai amfani alumma nan da shekarar 2030

Yace; Majalisar Dinkin Duniya tana kara kira ga Gwamnatin data kara himma wajen agazawa yan gudun hijira da marasa galihu dake rayuwa cikin kunci.

Sanan da matsalolin a vangaren Ilumi masamman ga yaran dake rayuwa a sansanonin yan gudun hijira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *