HUKUMAR ABINCHI TA DUNIYA TA KOYAR DA MATA DABARUN SARAFA ABINCHI MAI GINA JIKI A EBONYI

Hukumar abinchi ta Duniya ta koyar da mata yadda zasu sarafa abinchi maigina jiki a Ebonyi

Daga Zubairu M Lawal

Taron qarawa juna sani da Hukumar kula da abinchi ta Duniya karkashin Jagorancin Majalisar Xinkin Duniya ta shirya a garin Abakilike dake Jihar Ebonyi , ya samu halartan kungiyoyin mata dabam dabam daga sasan Nijeriya .

Taron ya samu hadin giwar kungiyar kasuwanci da cigaba ta Duniya tare da Bankin  IBTC da kuma Hukumar kula da Abinchi ta Duniya da sauran kungiyoyi.

Da yake jawabi a wajen taron Gwamnan jihar Ebonyi Injiniya Engr. Dave Umahi wanda  Dakta  Eric Igwe ya wakilta yace; Gwamnatin jihar Ebonyi tayi farin ciki  da wanan taron da aka gabatar a Jihar ta .

Kuma tayi murna da yadda taga ana koyar da mata sana’o’i kala dabam dabam masamman wadan da suka shafi fannin sarafa abinchi.

Gwamnan yace; wanan sana’o’in da ake koyar da matan Nijeriya taimako ne ga Gwamnatin qasa. Saboda mata masu sana’ar sayar da abinchi dama masu dafawa domin bukatuwar kan su, zasu amfana kuma su amfanar dana kasa dasu.

Yace; a yanzu haka qasan nan ana wahalar ayyuka  komai ana samun shi da wahala. Idan matan da ake koyarwan zasu mai da hankali kan abin da ake koyar dasu zasu ci riba , domin sun samu hanyoyin Sana’a ta yadda kudade za su riqa shugowa masu.

Ya qara da cewa wadanda suka samu wanan horon zasu mallaki takardan shedar zama kwararu a harkan kasuwanci mai dorewa.

Taron da ya gudana a zauren taro na Royal dake garin Abakaliki , uwargidan Gwamnan jihar Misis Rachel Umahi tace; Wanda ya koyar da kai Sana’a ya gama maka komai. Kamar ace wanda ya koya maka kama kiffi ,yafi ace kullun yana dauko kiffi yana ba ka.

Yanzu wanan Sana’a ya shiga kwakwalwar ku , kuma nan gaba zaku koyar ma na baya.

Da take tsukaci Shugaban mata ta Nijeriyi a kungiyar gamayyar Afirika Misis Comfort Lamptey, tayi kira ga mata dasu zama masu tausayi da jin kai .

Su rika koyar da yara sana’o’in hannu tun suna qanana . Tace kada suyi wasa da karatun yara da kuma batun Sana’a.

Kada yara su gama karatu babu aikinyi yakan janyo damuwa ta kowani hanya .

Kwamishiniyar harkokin Noma da albarkatun qasa ta jihar Ebonyi Misis Mercy Chukwu, tayi kira ga mata dasu riqa koyar da yaransu mata sana’o’in hannu da kuma girke girke.

Su kuma riqa sanya ido kan mu’amalar su ta yau da kullun. Tace Sana’ar noma ba sai lallai na miji ba .mata suna taka rawa a harkan noma .

Hoto na farko Shugaban Hukumar kwallon kafa ta jihar Nasarawa

Hoto na biyu kungiyar Nasarawa state first unity Forum

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *