LABARIN DA BA AJI BA A DUNIYA – COVID 19 MUTUM 1,300 SUN MUTU A KASAR AMURKA

LABARIN DA BA AJI BA A DUNIYA – COVID 19 MUTUM 1,300 SUN MUTU A KASAR AMURKA

An tattaro cewa zuwa yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar a Amurka ya kai 85,500, shafin BBC Hausata ruwaito.

Wasu sabbin alkaluma da jami’ar Johns Hopkins University ta tattara sun nuna Amurkar ta wuce China da kimanin 4000.

China dai na da wadanda suka kamu da cutar 81,782, inda a baya Italiya take rufe mata baya da 80,589.

To sai dai har kawo yanzu, China da Italiya na gaba da Amurkar wajen yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar ta coronavirus, inda mutum 3,291 suka mutu a China yayin da kuma 8,215 suka mutu a Italiya sannan Amurka ta rasa mutane 1,300 sakamakon wannan annoba.

Wannan karuwar yawan alkaluman na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da shugaba Donald Trump ya sanar da cewa kasar tasa ba da dadewa ba za ta yaki cutar coronavirus.

A gefe guda, mun ji cewa Matakan hana yaduwar muguwar cutar coronavirus da gwamnatin tarayyar Najeriya ke dauka a kasar nan suna da yawa ,kuma a halin yanzu har sun kai gidajen gyaran hali.

A cikin wannan kokarin ne gwamnati ta bada umarnin cewa a saki wadanda ake kan shari’arsu amma ake garkame dasu a gidajen.

Kamar yadda ministan lamurran cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana, an yi hakan ne don hana yaduwar cutar a gidajen gyaran hali.

Aregbesola ya bada wannan umarnin ne a yayin wani taron gaggawa da ya kira a ofishinsa a Abuja a kan yadda za a hana yaduwar cutar a gidajen gyaran hali.

Bayan taron ne ministan ya fitar da takarda wacce aka mika ga manema labarai ta hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Mohammed Manga, inda ya ce wannan umarnin ya biyo bayan hukuncin kwamitin fadar shugaban kasa na yakar cutar ne.

Ya kara da cewa an dauka matakan ne don kare masu zama a gidajen gyaran halin, ma’aikatansu da kuma sauran ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *