ME YAYI ZAFI – YA’YAN JAM’IYYAR PDP SUN BUKACI UWAR JAM’IYYAR TA SAUKE FRANCIS OROGU NA JIHAR NASARAWA DAGA SHUGABANCI

Anyi kira ga uwar jam’iyyar PDP ta qasa da ta sa baki kan abin da ke faruwa a Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gungun matasan jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa sunyi kira ga uwar jam’iyyar ta qasa da ta sanya baki kan abinda ke faru cikin jam’iyyar a Jihar.

Ga mayyana matasan jam’iyyar PDP da suka fito daga gurare dabam dabam cikin Jihar Nasarawa sunyi kira ga shugaban jam’iyyar PDP ta jihar Hon.Francis Orogu daya tattara nashi yi nashi ya bar Jagorancin jam’iyyar.

Da yake karanta qasidar gaban manema labarai Honorabul Devid yace; dakayarewar da akayiwa Manyan jagororin Jam’iyyar PDP da ake gadara dasu a Jihar Nasarawa bai dace ba.

Ya qara da cewa Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar kuma Tsohon Minista kuma Tsohon Sanata mai wakiltar mazaver Nasarawa ta Arewa Sanata Solomon Ewuga da Honorabul Musa Elayo da Tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jihar Nasarawa kuma Tsohon Xan Majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Mazaver Doma da Keana da Awe, Honorabul Muhammad Ogoshi Onawo, sun fi Honorabul Francis Orogu jama’a nesa ba kusa ba a Jihar Nasarawa.

Saboda haka batun yace ya dakatar dasu daga jam’iyyar PDP bai taso ba .kuma babu wani Shugaban jam’iyyar PDP daga qananan Hukumomi da ya goyi bayan wanan xanyen aiki da Orogu yayi.

Cikin takardan an zargi Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar dayin halin ko in kulla cikin halin da jam’iyyar PDP ta shiga a babban zave ta 2019.

Yace Honorabul Orogu yayi banza da jam’iyyar lokacin da ake tayi mata magudi ana kwace kujerun da jam’iyyar tayi nasara a lokacin zaven .

Yace; yayi kwanciyar sa a gida bai damu da ko jam’iyyar tayi nasara ba. Kuma kudaden da aka baiwa jam’iyyar saboda yakin zave Shugaban jam’iyyar yayi kwanciyar sa akan kudin .

Hakan yasa jam’iyyar ta rasa kujeran Sanatochi uku sanan ta rasa kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya guda uku duk da cewa jam’iyyar ce tayi nasara amma da hadin bakin Shugabnata akayi mata karfin tuwo aka kwace amma bai iya cewa ko mai ba.

Haka zalika Honorabul Orogu ya kasa kawo akwatin Mazaver sa dana gundumarsa duk da cewa a baya ya taba wakiltar Mazaver a Majalisar dokokin Jihar Nasarawa.

Wanan alamin tambaya ce meyasa yanzu PDP ta kasa kawo Mazaver Shugaban ta na Jihar Nasarawa?. Saboda Shugaban ya rike komai kudaden da aka kawo domin aiki a zaven Shugaban qasa boye ,mai makon 300,000 da aka ayyana za a raba a kowani akwati. Sai Orogu ya riqa raba 150,000 .

Shugaban jam’iyyar PDP Honorabul Orogu ya taimakawa jam’iyyar APC wajen samun nasara ta hanyar magudi a zaven 2019 a Jihar Nasarawa.

Yanzu yana kokarin qara rushe jam’iyyar saboda manyan jam’iyyar sunce basu yarda da abubuwan da yake yi ba ,ya mai da jam’iyyar tankar nashi shi kadai ,hakan yasa yace ya koresu .

Tawagar matasan jam’iyyar PDP ta jihar Nasarawa sun bukaci uwar jam’iyyar data takawa Shugaban na Jihar biriki sanan a gudanar da zave na gaskiya, saboda gudanar da gaskiya shine zai baiwa jam’iyyar damar samun nasara a zave na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *