TAZARAR HAIHUWA TSARI NE DAKE BAIWA IYAYE SAMUN CIKAKEN LAFIYA TARE DA YA’YAN DA AKE RENO

TAZARAR HAIHUWA TSARI NE DAKE BAIWA IYAYE SAMUN CIKAKEN LAFIYA TARE DA YA’YAN DA AKE RENO

Awwal Umar Kontagora

Tazarar haihuwa tsari ne da ke anfani wajen samar da ingantaciyar kiwon lafiyar uwa da kuma samar da tazara tsakanin ya’ya wanda yake da anfani a tsarin iyali.

Jama’a da dama na kallon wannan tsarin tamkar tsari ne na ko karin takaita iyali wajen samun ya’ya, wanda kuma da dama an jahilci tsarin, domin tsari da ke baiwa uwa damar samun damar yin raino yadda ya dace ta hanyar kula da lafiyar yara da kuma kaucewa yin haihuwar rurrutsa wanda da dama kan jefa uwa cikin halin kakanikayi da wani lokacin kan haifar da samun yara marasa kwazo ta dalilin rashin samun kulawar da ta dace daga uwa. Ita kan uwar yin rurrutsa a wajen samun iyali kan haifar mata rashin kuzari da ingantacciyar lafiya a jikinta.

Tsarin dai yana da alfanu idan bi shawarwarin masana kiwon lafiya, domin akwai matakan da ake anfani da su wanda wasu malaman addini ma sun amince da shi da har an samar da hanyoyin anfani da wannan tsarin a shari’ance.

Sau da dama yanayin yadda tatralin arziki ke tafiyar hawainiya kan taimaka wajen rashin samun damar baiwa yara masu tasowa kulawar da ta dace da a karshe kan hana samun damar baiwa yara ilimi mai inganci tare da rashin samun kulawar iyaye musamman maza wajen sauke nauyin da ya rataya akan su na kula da lafiyar yara da basu damar rashin kulawa da yanayin rayuwarsu na yau da kullun.

Wannan tsarin masana kiwon lafiya na yekuwa akan sa tare da bada shawarwari ga iyalai musamman ganin yadda duniya ta karkata wajen ganin kafin wani wa’adi an samu yara masu tasowa su kasance masu kwazo da ingantacciyar tunanin da za ta ba su damar fadada tunanin su wajen inganta tattalin arzikin su ta yadda zasu samu ingantacciyar rayuwa.

Muhammadu Turaki, masani ne a bangaren kiwon lafiyar iyali, yace tazarar haihuwa hanya ce da kan taimaka wajen baiwa yaya tazara ta yadda za a rika samun tazara a tsakanin su ta yadda na gaba zai iya samun damar kulawa da wanda ke biye da shi, yayin da ita kan ta uwa za ta iya samun damar kulawa da lafiyarta sabanin yadda ake haihuwar rurrutsu da a wani lokacin kan haifar da matsalolin rashin lafiyar uwa, saboda damuwa kan matsalolin tarbiyar yara kanana, saboda haka akwai bukatar magidanta su rika ziyartar cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa da su da neman shawarwarin masana kiwon lafiya akan matsalolin tazarar haihuwa saboda yanzu akwai kayan aiki kuma akwai masana kan tsarin tazarar haihuwa a kowace cibiyar kiwon lafiya musamman mallakin gwamnati.

Likitan ya kara da cewar lokaci yayi da ba sai an nusar da magidanci akan tazarar haihuwa ba duba da irin yadda tattalin arziki ke tafiyar hawainiya da yasa da daman iyaye ba sa iya daukar nauyin yayansu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *