AN SAMU MASU CUTAR COVID-19 WADANDA AKA KILLACE SUNA LALATA DA JUNA

An samu wasu daga cikin wadanda aka killace a wajen ajiye masu dauke da COVID-19 na lalata da junansu – Gwamnati
Wani abin mamaki da ban takaici shi ne na wani rahoto da ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda gwamnati ta killace sakamakon samunsu dauke da kwayoyin cutar Coronavirus sun buge da neman juna ta fuskar lalata a inda gwamnati ta ware don killace wadanda suka harbu a kasar Uganda.

Jaridar WatchDog Uganda ta rawaito cewa sakatariyar dindindin ta ma’aikatar lafiya ta kasar Uganda, Diana Atwine ce ta tabbatar da faruwar wannan lamari a yayin wata hira da ta yi da gidan rediyo a wani shiri mai taken One Talk Show.

A cewar sakatariyar ta ma’aikatar lafiya, Diana, ta ce, gwamnatin Uganda ta karbi otal-otal ne don killace wadanda aka tabbatar sun harbu a johohin kasar don killace su, amma abin takaici sai ga shi da dama daga cikin wadanda aka killace su din suna barin dakunansu suna komawa dakunan mata ko maza masu dauke da COVID-19 suna aikata lalata da junansu.

Diana ta bayyana cewa wannan lamari na matukar ci wa ma’aikatar lafiya ta Uganda tuwo a kwarya kasancewar lamarin na lalata shirin gwamnati na kawar da cutar daga kasar.

“Ugandans are not serious. Some who are in quarantine have even begun having (sexual) affairs. They move to rooms of others in the hotels where we have placed them.

“Mutanen Uganda sam basu da kirki, wasu daga cikin wadanda aka killace sun fara yin lalata da junansa a inda aka killace su.

“Mun samu wasu a yankin Mulago da aka kebe a otal sun bar dakunansu sun koma dakunan makwabtansu a cikin otal din sun kulla abota har sun fara yin lalata da juna alhalin suna jinya.

“Wannan sam babu tsari, kuma zai zama cikas ga burinmu na dakile cutar kafin ta ta’azzara,” inji Diana.

Gwamnatin Uganda dai ta ware otal-otal guda 17 a fadin kasar a matsayin wajen killace masu dauke da cutar COVID-19

Zuwa yanzu dai akwai akalla mutane 232 a killace a Uganda, inda gwaji ya tabbatar da cea mutane sama da 50 na dauke da cutar, kuma zuwa yanzu mutane 7 sun warke har an sallame su

Wadannan ra’ayoyi da aka wallafa a wannan rubutun na wanda ya rubuta ne, Ba ra’ayin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *