KILLACE AL’UMMA A GIDAJE SABODA CUTAR COVID-19 ZANGA -ZANGA TA BARKE A GARIN JOS

KILLACE AL’UMMA A GIDAJE SABODA CUTAR COVID-19 ZANGA -ZANGA TA BARKE A GARIN JOS

Daga Wakilinmu

A safiyar Yau ne dubban mata suka fito kan tituna kwai da kwarkwata Musulmai da Kirista su na zanga-zanga a Jos, wanan zanga zangar ta biyo bayan halin da suka shiga na rashin abinci da na sha saboda alkawarin da gwamnatin jihar ta ki ciki musu na raba musu kayan rage radadin yunwa sakamakon killace su da akayi a gida saboda Korona bairos.

Masu zanga zangar dauke da kwalaye da ganye suna fadin Korona bata kashe mu ba yunwa zai kashe mu . Sun tare hanyoyin Farar Gada, Sabon Stadium da Mil bakwai, kuma sun ce ba za su tashi ba sai an kawo musu abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *