MATA SUNA BA DA GUDUMAWA WAJEN YAKI DA CUTAR COVID-19 A DUNIYA

Mata suna ba da gudumawa wajen yaki da cutar Korona bairos a duniya

Inji Mista Edward

Daga Zubairu Lawal

Da yake jawabi Babban jami’i a fannin yada labarai na Majalisar dinkin Duniya dake birnin Ikko Mista Edward  Kallon ya ce , hakiqa mata suna bada gudumawa kashi 70% cikin 100% wajen yaki da annobar cutar Korona bairos a duniya.

Ya ce , a cikin kungiyoyin Likitochi na Duniya akwai mata kuma kowa na ganin irin rawar da suke takawa wajen ganin masu fama da citar sun samu sauki .

Saboda haka dole a jin jinawa iyaye mata domin sun cancanci yabo.yanzu cikin hukumar yaki da qazanta na qasar mu Nijeriya (NCDC) akwai mata da dama da suke aikin ceton rayukan dubbannin al’umma.

Taken taron an gabatar da shine domin nuna rawar da mata ke takawa wajen yaki da annobar cutar Korona.

Sannan aka bukaci masu mugun nufi na cin zarafin mata da su dai na saboda an zama daya kuma mata na bada gudumawa ta kowani fanin na rayuwa.

Ya ce  kamata ya yi a wannan lokacin na Cutar Korona bairos  a kawo karshen cin zarafin mata a fadin Duniya baki daya.

Saboda a wannan lokacin mata na matukar ba da gudun  mawa,  saboda akwai likitoci da yawa a cikin su, kuma suna ba da gudunmawa wajen warkar da masu cutan korona din.

Dan haka ba wani bambacin wajen ba da gudunmawa a tsakanin Maza da Mata a wanan lokacin da Duniya take bukatar duki ta ko ina.

Taron da ya gudana a zauren tattauna matsalolin da suka addabi duniya, ya janyo hankalin al’umma dasu kara yabawa iyaye mata saboda taimakon su ya fi na maza yawa a wanan lokacin.

Mata sun taimaka wajen tsare yara a gida sun kuma dauki nauyin tsaftace muhalli da hannayen yara da karesu daga shiga guraren da zasu iya dauko cututuka .

Haka zalika sun taimakawa mazaje wajen kwantar masu da hankali saboda zaman gida ba domin komai ba sai domin kariya daga annobar cutar Korona.

Gwamnatin Lagos ta yabawa wa mata saboda jajircewa masamman kungoyoyin mata masu zaman kansu da suka rika wayar wa al’umma da kai saboda illar wanan cutar.

Taron ya kara tabbatar da cewa za a kara daukar kwararar matakai wajen duk Wanda aka samu da cin zarafin mata koda matar sa ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *