MUTANIN AWE DOMA KEANA SUN AMFANA DA TALLAFIN ABINCI NA 13 MILIYON DAGA HASAN NA LARABA

MUTANIN AWE DOMA KEANA SUN AMFANA DA TALLAFIN ABINCI NA 13 MILIYON DAGA HASAN NA LARABA

Daga Zubairu Lawal Lafia

Dan Majalisar tarayya mai wakiltar mazaver Doma da Awe da keana  Hon. Abubakar Hasana na Laraba  ya bawa al’umman mazaver shi kayan abinci  da yawan shi ya kai naira miliyon 13.
Cikin. Kayyakin abinci da suka hada da buhun shinkafa mai nauyin keji 25 guda 1,200 da Doya guda dubu uku . jimillar kayan ya kai naira miliyon goma sha uku.

Da yake zantawa da manema labarai Honorabul Abubakar Hasan na Laraba  ya ce , wannan kayan abincin an bada shine saboda halin da ake ciki na matsalar cutar Korona bairos.

Ya ce ,yanzu al’umma suna cikin halin kunchi saboda an kulle gari an zaunar da mutani a gida , saboda gudun yaduwar cutar Korona.

Ya qara da cewa ga shi an fara Azumin Ramadan al’umma suna  bukatar tallafin gaggawa. Ya ce mun ba da tallafin Shinkafa buhu 1200 da Doya dubu uku ga qananan hukumomi uku da muke da su a mazaver mu .

“Muna da gundumomi guda 30 a mazaver mu , muna bukatar a rabawa  al’umman mazaver mu “.

Ya ce , abubuwan da mukayi na tallafin muna fatan ya kai ga al’umman mazaver mu, muna godiya ga Gwamnatin tarayya da Gwamnatin jihar saboda taimakawa al’umma.

Na Laraba yayi kira ga masu rabon wanan kayan tallafin da su ji tsoron Allah suyi adalci su duba rayuwar talakawa da halin da Talakawa ke ciki.

Ya qara da cewa Wanan kayan da muka bada munsan kayan abinci yana tsada kuma kayan zai kai naira miliyon goma sha uku.

Dan Majalisan yayi kira ga al’umman mazaver Doma da Awe da Keana , da cewa su kiyaye saboda wanan cutar ta Korona bairos gaskiya ne .

Ya ce , daga makon da ya wuce zuwa wanan makon an samu asarar rayuka mutani sama da dari shida a kano. Saboda haka muyi adu’a wanan cutar bai zo nan ba mu roki Allah kada ya shigo mana jihar.

Saboda mu Nijeriya bamu da kwarewar Asibitochi irin qasa shen Amurka da Italiya da Sipen mun ga yadda suka riqa mutuwa duk da kwarewarsu wajen kiwon lafiya .

Saboda haka al’umma su guje cudanya tsakanin alumma wanan matakin da Gwamnati ta dauka na takaita zurga zurga yana da kyau.

Mu kiyaye mu natsu waje daya saboda cutar yana yawo ne a isaka . mu riqa tsaftace hannaye da muhali inji Hasan Na Laraba.

Cikin wadanda suka amfana da wanan tallafin sun nuna jin dadi da sanya albarka .

Honorobul Yusuf Dogara daga qaramar hukumar Awe ya bayyana jin dadinshi da wanan tallafin. Ya ce , halin da ake ciki yanzu al’umma suna bukatar tallafin gaggawa.

Ya ce na wakilce Shugaban qaramar hukumar Awe da alumman Awe kuma zamu kai masu suma suyi murna da godiya da sanya albarka.

Kuma zamu kai mu rabawa al’umma wanda ya samu ya samu zamuyi dai dai gwargwadon iya wanmu.

Shima Mista Tomos Ogiri wanda ya wakilci al’umman qaramar hukumar Doma ya yabawa Honorabul Hasan Na Laraba saboda yadda ya taimakawa al’umma mazaver shi.

Ya ce , Wanan tallafin da Na Laraba ya ba al’umma ya basu a lokacin da ya dace ga matsalar cutar Korona bairos ga Azumin Ramadan. Ya ce zasu rabawa al’umma duk da cewa ba kowa ne zai samu ba amma zasu raba zuwa kan wanda ya samu.

Shima Shugabañ Qaramar hukumar Keana  Honorabul Adamu Adi Sardaunar Giza ya yabawa tallafin Xan majalisar. Ya ce aikin alherin da Dan Majalisan yayi abin godiya ne saboda halin da al’umma suke ciki .

Ya ce , muma a nan qaramar hukumar Keana muna kokarin yaki da cutar mun sanya jami’ai a kan iyakoki suna tantance duk Wanda zai shigo . muma da abubuwan gwaji da wanke hannaye kafin a shigo qaramar hukumar Keana.

Ya qara da cewa muna kokari wajen magance matsalar tsaro domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a qaramar hukumar Keana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *