A KARON FARKO – JIHAR NASARAWA TA SHIGA JERIN MASU CUTAR COVID-19

A KARON FARKO – JIHAR NASARAWA TA SHIGA JERIN MASU CUTAR COVID-19

Daga Zubairu Lawal

Duk da kokarin da Gwamnatin jihar take yi na ganin cutar bai samu ma tsuguni gun alumman jihar Nasarawa ba amma a ranar Littinin aka tabbatar da wata baiwar Allah ta kamu da wannan cutar .

Wadda ta kamu da cutar ta na zaune ne a karamar hukumar Kokona cikin jihar Nasarawa.

Da yake zantawa da manema labaria bayan taron tabbatar da tsaro da yaki da cutar Korona bairos a cikin jihar.

Kwamishinan kiwon Lafiya ta jihar Dakta Ahmad Baba Yahaya ya shedawa manema labarai ce wa yanzu haka wadda aka samu da cutar tana kwance a cibiyar bada lafiya da Gwamnatin jihar ta ware saboda masu cutar Korona bairos a Shabu cikin birnin Lafia.

Kuma Gwamnatin jihar zata cigaba da kulawa da ita har sai ta samu lafiya .

Shima Sarkin Keffi Alhaji Chindo YaMusa ya tabbatar da dokar da Gwamnatin jihar ta sanya ce wa za a iya kiran Sallah amma a shiga gida ayi Sallah.

Kwamishinan yada labarai Kwamared Doga Dan Ladi Shama ya kara jaddada aniyar Gwamnatin jihar na takaita zurga zurga .

Ya kuma ce tallafin da Gwamnatin jihar Nasarawa ta baiwa mutanin jihar. Akwai na Gwamnatin tarayya ya nanan tafe. Sannan akwai kayan abinci da wasu yan jihar suka bayar da tallafi za a rabawa al’umman jihar nan ba da dadewa ba.

Kwamishinan yan Sandan jihar Emmanuel Lolon ya ce an kara tattauna kan batun takaita zurga zurga cikin jihar daga shida zuwa takwas.

Ya ce , a baya rundunar jami’an tsaron hadin giwa karkashin Kwamishinan yan sandan jihar sun kama sama da mutum dari hudu .

Kwamishinan shari’a ta jihar Barista Kana ya ce , Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya tabbatar da dokar hana hawa mashin da goyo da kuma Adaidaita sahu, wato keke Napel. Duk Wanda aka kama yayi kuka da kansa.

Sannan ya bayyana ce wa daga zuwa gobe ne Gwamnatin jihar Nasarawa zata fara mai da yaran almajirai zuwa garuruwan su.

Sannan za a rufe dukkanin kasuwan dake qaramar hukumar Karu wanda ke makwaftaka da birnin tarayyar Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *