CUTAR COVID-19 YAFI ILLA GA MUTANI MASU YA WAN SHEKARU A DUNIYA

CUTAR COVID-19 YAFI ILLA GA MUTANI MASU YA WAN SHEKARU A DUNIYA

Inji Sakataren MDD

Daga Zubairu M Lawal

Cutar Korona bairos ya fi yin illa ga mutani masu shekaru mai ya wa , masamman tsofafin masu shekaru daga saba’in zuwa tamanin da sauran su.

A wani bincikenda manyan likitochin duniya suka gabatar ya nuna cewa wadanda suka fi mutuwa a wannan Annobar cutar Korona bairos manyan mutanine masu dogon shekaru .

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya mista Antonio Guterres ya bayyana haka a wajen taron gano matsalolin da wannan Annobar cutar Korona bairos ta haddasa.

Ya ce a duk kanin qasashen duniya da Annobar cutar tayi illa sa sai zakaga manyan mutani ne masu yawan shekaru ta fi yi masu illa.

Ya ce  sakamakon cutar idan ta shiga jiki ta tarar da wani cuta to tana hadewa ne . saboda haka take illa ga manyan mutani sakamakon aka sarin manyan mutani baka rasa su da yan cututtuka kamar ciwon shuga , hawan jini da tarin fuka da asma da ciwon koda ko hanta da sauran su.

Shiyasa cutar Korona bairos ke samun damar illata manyan mutani farar daya sabanin yara masu matsa kaicin shekaru .

Mista Antonio Guterres yayi kira ga alumman Duniya da su rika kiyayewa su dauki shawar da likitochin Duniya suka ba da saboda rage yaduwar cutar cikin al’umma.

Ya ce , rage zurga zurga da cin koso da yawan wanke hannaye suna cikin rage yaduwar cutar cikin al’umma.

Sannan ya shawarci manyan mutani masu yawan shekaru da su kasance masu yawan ziyartan Asibitoci akan lokaci domin ya wan duba lafiyar su da zarar mutum ya ji ba dai dai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *