SAMAR DA SANA’O’IN HANNU GA MATASA ZAI BUN KASA TATTALIN ARZIKIN KASA

SAMAR DA SANA’O’IN HANNU GA MATASA ZAI BUN KASA TATTALIN ARZIKIN KASA

Inji Cynthia Samuel

Daga Zubairu M Lawal

Mista  Cynthia Samuel-Olonjuwon  shine Babban Jami’i  a fannin inganta tattalin arziki a kungiyar Nahiyar Afirka ya ce a halin da ake ciki yanzu tattalin arziki ya zama koma baya sakamakon rashin aikinyi ga miliyoyin mata dake zaman kashe wando a wannan Nahiyar.

Mista  Cynthia Samuel-Olonjuwon ya bayyana haka ne a taron samar da mafita na rayuwar matasa yan Nahiyar Afirka. Wanda ya samu hadin giwa na kungiyar Kwadago ta ILO da ITU suka shirya.

Mista  Cynthia Samuel-Olonjuwon  ya ce , akwai hanyoyin fasaha ta zamani wanda matasan da suka samu ilumin kimiyya da fasaha zasu amfana da shi a ko ina.

Ya ce , amma sakacin Gwamnatoci babu wannan hikimar na taimakawa rayuwar matasan , ta irin wannan hanyoyin da zai inganta rayuwar su da iyalan su.

Ya ce , ba sai matasan da sukayi karatu sun samu aikin Gwamnati na zaman ofis ba.

Idan Gwamnati ta taimakawa matasa masu hazaka da cibiyoyin koyar da sana’o’in kire-kire miliyoyi dake koyan zasu amfana kuma Gwamnati zata rika samun kudaden shiga ta wannan bangaren.

Taron da ya gudana na yini biyu a birnin Abuja ya mai da hankaline kan yadda za a kawo kar shen zaman kashen wando da matasa ke yi , kafin nan da shekarar 2030.

Ya ce Majalisar Dinkin Duniya kullun damuwar ta yana yin rayuwar matasa da basu da ayyukan yi. Ya qara da cewa rayuwar matashi ya fi kowani rayuwa hadari . saboda idan matashi ba shi da aikinyi to yana iya shiga kowani hadarin rayuwa da zai samar masa da kudi.

Wajibi ne Gwamnatocin Nahiyar Afirka su kara hada kai su samu tallafi daga hadin giwar Majalisar Dinkin Duniya domin samar da sana’o’in hannu na zamani da zai taimakawa rayuwar matasa.

Taron da ya samu halartan wakilan kasa she biyar daga Nahiyar Afirka da suka hada da kasar  Cote
d’ Ivoire, Kenya, Nigeria, Rwanda, Senegal da South Africa.

A nasa jawabin Ministan harkokin Kwadago Nijeriya Honorabul  Chris Ngige, ya ce , yanzu haka Gwamnatin Nijeriya tayi nisa wajen tsare tsaren samar da wannan mafita ga rayuwar matasa . aka sarin gurare sun fara cin moriyar shirin da akeyi na (ICT) wannan an samar ne  saboda cigaban matasa .

Ya qara da cewa Ma’aikatan kungiyar Kwadago da ma’aikatan Matasa  da wasanni na qasa suna tattauna wannan ba tun, na samar da mafita da zai inganta rayuwar matasa da sana’o’in hannu na zamani, maimakon dogaro da aikin Gwamnati wanda mutum bai da tabbas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *