YAN JARIDA SUN BA DA BABBAN GUDUMAWA WAJEN YAKI DA CUTAR COVID-19 A DUNIYA

YAN JARIDA SUN BA DA BABBAN GUDUMAWA WAJEN YAKI DA CUTAR COVID-19 A DUNIYA

Inji Mista  Guterres

Daga Zubairu M Lawal

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio Guterres ya yabawa yan jarida kan babban gudumawar da suka bada wajen yaki da cutar Korona bairos a Duniya.

Mista Antonio Guterres ya ce , babu misaltuwa irin kokarin da yan jarida keyi a wannan lokacin da Duniya ta shiga rudani na Annobar cutar Korona bairos.

Ya ce , Gudumawa yan jarida ya sanya alumman Duniya suka fahinci halin da ake ciki na mace-mace da cutar Korona ke haifarwa.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana haka ne a bikin ranar yan jarida ta Duniya wanda ta gabata ranar 3 ga watan mayuh na shekarar 2020.

Mista  Guterres ya ce , damar da aka ba yan jarida na yin bincike da fadin abubuwan da suke gani ya amfanar da al’umma wajen samun ways wan kai.

Ya ce , yan jarida sun binciko yadda mutani ke mutuwa ake gudanar da jana’izarsu ba bisa tsarin yadda ake gudanar da jana’iza ba saboda illar yaduwar cutar.

Qasashen da annobar cutar tayi muni yan jarida sun riqa yada yadda ake fama da matsalar yaki da cutar. Kuma sun wayar da kan al’umma saboda matakin da Gwamnatochin Duniya suka dauka na killace al’umma.

Sakataren yayi kira ga Shugabannin qasashen duniya dasu riqa baiwa yan jarida damarsu na yin aiki kamar yadda tsarin mulki ya basu.

Sannan ya bukaci Shugabannin su riqa taimakawa yan jarida wajen kare lafiyan su a duk lokacin da suke bakin aiki.

Ya kuma nuna takaici da yadda ake cin zarafin yan jarida a wasu gurare masamman lokacin da suke daukar labari.

Sannan yayi kira ga yan jarida da su riqa gudanar da sahihiyar bincike da tabbatar da labari mai inganci da labaran hadin kan jama’a .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *