CUTAR COVID-19 – YAN MAJALISAR JIHAR NASARAWA SUN TSELLAKE RIJIYA DA BAYA

CUTAR COVID-19 – YAN MAJALISAR JIHAR NASARAWA SUN TSELLAKE RIJIYA DA BAYA

Daga Zubairu M Lawal

Bayan mutuwan daya daga cikin yan Majalisar dokokin jihar Nasarawa guda 24 . Aka ummurci 23 da su killace kawunan su Sannan akayi masu gwajin kwayar cutar Korona bairos.

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya bayyana cewa sakamakon gwajin kwayar cutar da akayiwa yan Majalisar ya nuna babu guda daya daga cikin su da yake dauke da cutar.

Saboda haka Gwamnan ya ce ya taya yan Majalisar dokokin jihar murna na samun wannan kyakyawar sakamakon.

Ya qara da cewa bayan kulle qaramar hukumar Nasarawa saboda tantance mutanin da sukayi ta’amali da tsohon Dan Majalisar da ya rigaye mu gidan gaskiya.

Gwamnan ya ce an samu karin masu cutar Korona bairos a jihar Wanda adadinsu ya kai goma sha uku.

Ya ce , hudu an samesu ne a jihar tara kuma an same su ne gun jama’an da suka shigo jihar daga jihohin Kano da Lagos.

Saboda haka Gwamnan ya ba da ummurinin a cigaba da killace qaramar hukumar Nasarawa domin cigaba da zakulo wadanda sukayi mu’amala da Adamu Sulaiman.

Gwamna Abdullah Sule ya yi kira ga alumman jihar Nasarawa da su riqa bada hadin kai ga tsare tsaren Gwamnati na yaki da cutar Korona bairos.

Haka zalika ya yabawa yan jarida  saboda rawar da suke takawa wajen fadakar da alumman jihar. Haka zalika ya yabawa jami’an tsaro saboda rawar da suke takawa wajen kare martabar jihar.

Ya zuwa yanzu masu dauke da cutar ta Korona bairos a jihar Nasarawa adadinsu ya kai 24 bayan guda daya da ya mutu .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *