KAR A MANTA DA NAKASASSU WAJEN TAIMAKON COVID-19 A DUNIYA

KAR A MANTA DA NAKASASSU WAJEN TAIMAKON COVID-19 A DUNIYA

Inji Antonio Guterres

Daga Zubairu M Lawal

Babban Sakataren Majalisar DInkin Duniya mista Antonio Guterres yayi kira ga Gwamnatocin Duniya da su taimakawa rayuwar Nakasassu dake rayuwa cikin kunci da talauci.

Mista Guterres ya qara da cewa a halin da ake ciki yanzu haka .
An tabbatar da cewa akwai mutane Nakasassu Biliyon daya a fadin Duniya.

Kuma an mayar da su saniyar ware a fadin Duniya a cikin Al’ummummu ba a tsinana komai tare da su. ko kafin shigowar cutar Annobar  Koronabairos  ba’a damu da kula da lafiyar su .

Har kokin  ilimin su da sana’o’in sune ci baya   cikin al’umma, ba’a kuma  daukar su aikin Gwamnati,  suna rayuwa ne a yanayi na talauci, kuma hakan na ingiza su su fada harkoki na ta’addanci.

Mista  Antonio Guterres ya ce   Gaskiyar magana ya kamata aba wadannan naqasassu kulawa ta musamman  a wannan yanayi na cutar covid-19, dan ya zama cewa suma an maida su kamar sauran mutane a cikin Al’umma a gaba dayan fadin Duniya

Ya qara da cewa a samar masu da harkokin sana’o’in da zasu dogara da kawunan su.

Bai kamata a maida su saniyar ware ba. Suma mutanine a cikin su akwai masu hazaqa da ilumi kuma suma zasu iya yin ayyukan cigaba kamar yadda kowa yake yi. Akwai sana’o’in hannu da Suke da hikimar sarafawa wanda zai amfani mutani .

Ya ce  suma Nakasassu suna taka rawa wajen yaki da Annobar cutar Korona bairos da ta addabi duniya.

Saboda suma suna yada manufofin su ga alumman suna fadakar da na kusa dasu.

Ya qara da cewa samar masu da ayyukan yi da zai taimake rayuwar su zai kara rage yawan masu zaman kashe Wanda babu aikin yi.

Kuma zasu guji aikata miyagun ayyuka koda aikin da zai basu makudan kudade ne . kuma ba zasu goyi bayan masu aikata miyagun ayyuka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *