GWAMNATIN NASARAWA TA MAI DA AL-MAJIRAI 1,706 ZUWA JIHOHIN SU NA HAIHUWA

GWAMNATIN NASARAWA TA MAI DA AL-MAJIRAI 1,706 ZUWA JIHOHIN SU NA HAIHUWA

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnatin jihar Nasarawa tabi sahun Gwamnonin Arewa wajen tura qananan yara da shekarun su bai dara goma ba dake almajiranci a jihar zuwa asalin jihohin su na haihuwa.

Bayan tantance al-majiran da yawan su ya kai kimanin 4796 gwamnatin ta fara jigilarsu tun daga makon jiya ranar lahadi 3/5/2020 zuwa 11/5/2020.

Duk da cewa sauran al-majiran da malamansu sunyi Batan dabo amma Gwamnatin ta samu damar kwasan 1,706 zuwa jihohin su na haihuwa.

Da take jawabi gaban al-majiran  da suka samu damar shiga motoci zuwa jihohin su. Shugaban Kwamitin shirin na  mai da al-majirai jihohin su. Kwamishiniyar harkokin Mata da walwala ta jihar Nasarawa Hajiya Halima Ahmad Jabiru.

Tayi godiya ga malaman da suka baiwa gwamnatin jihar hadin kai wajen ganin an mai da kananan yara yan kasa da shekaru goma zuwa gaban iyayen su.

Tace da su ayau lahadi Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule bai samu zuwa ba. Saboda haka ya wakiltani nayi maku jawabi . Ku sani ba wai Gwamnan ya koreku ba ne a jihar shi.

Shekarunku ne sukayi qaranci ya kamata ace ya zuwa yanzu kuna gaban iyayen Ku. Ta ce  a wannan lokacin da ake fama da barazanar Cutar Korona bairos wanda ta addabi duniya.

Wannan lokacin da aka rufe gari malami daya ba zai iya kulawa da al-majirai zama da 100 a gaban shi ba.

Kuma yanzu cutar tana qara bunqasa ba a fuska cutar take ba bare a gane mai ita.

Tana iya yuhuwa wanda zai ba ku sadaka yana dauke da cutar da zarar kunyi mu’amala da shi sai ku kamu da cutar. Sannan miyagu suna samun dama wajen sace qananan yara ko kuma suyi amfani da su wajen ayyukan cutarwa da suke yi.

Ta kara da cewa a irin wannan lokacin da ake ciki Malaman Ku ba zasu iya kulawa da ku ba kamar yadda iyayen Ku zasu iya kulawa da ku.

Kwamishiniyar ta ja kunnin al-majiran da su kula da karatu a gaban iyayen su. Su zama masu ladabi da biyyaya . sannan ta bukaci iyayen yaran da su sanya su suyi karatun boko su hada duka biyu .

Ta ce yanzu Duniya ta sauya dole sai an hada ilumi Bangaren biyu saboda nan gaba yaran nan sune Shugabanni idan ba suyi ilumin boko ba sai su zama bayi .

ya zama masu dole su nemi ilumi tun suna qanana bai kamata a rika tura yara qanana suna zuwa yawon bara a kan tituna ba . Hakin kiyaye ne su kula da tarbiya da karatun yaran su.

Shima da yake jawabi Malam mai babban Allo ya ce wannan shirin da Gwamnati tayi yayi dai dai saboda yanzu zamani ya sauya .

Halin da ake ciki a gaskiya Malamai ba zasu iya kulawa da rayuwar yara qanana da suke gaban su ba . yanzu Annobar cutar Korona bairos ta suya yana yin Duniya kowa na ta kai ta kai , gara iyaye sune zasu kula da rayuwar su.

Saboda abinda za a ci yanzu ya zamo damuwa an kulle gari yaya yaro zai yi babu kasuwa masu bada sadakanma suna fama.

Suma yara qananan da suka samu kansu cikin tawagar da zasu koma garin su na haihuwa suna bayyana jin dadinsu kamar haka.

Yaro Xan kimanin shekara biyar mai suna Abbas Salisu wanda ya fito daga garin Taura dake jihar Jigawa ya bayyana farin cikin sa na cewa zaije yaga Babbarshi. Da aka tambayeshi inane jihar su yace Taura , yaushe kukazo jihar Nasarawa yace jiya , kuma ma baisan sunan Malamin su ba.

Duk da cewa yana da qarancin shekaru amma ya kasance cikin murna . shima Muhammad wanda ya ce shi Dan jihar Katsina ne kuma shekarun su hudu a Nasarawa yana murna yanzu zaije yaga iyayen shi.

Shima Abubakar Muhammad wanda yazo daga jihar Bauchi yayi godiya ga Gwamna Abdullah Sule yace shekarun shi biyu a Nasarawa bai taba ganin iyayen shi ba , yana bukatar ganin su , kuma zai yi karatun boko  idan ya koma gaban iyayen shi.

Shima Annas wanda ya zo daga Kano yace zai gayawa iyayen shi su sanya shi a makarantar boko .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *