UWARGIDAN GWAMNAN NASARAWA DA KWAMISHINIYAR HARKOKIN MATA SUN RABA KAYAN ABINCI

UWARGIDAN GWAMNAN NASARAWA DA KWAMISHINIYAR HARKOKIN MATA SUN RABA KAYAN ABINCI

Daga Zubairu M Lawal

Uwargidan Gwamnan jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullah Sule tare da hadin giwar gidauniyya Halima Jabiru gausiyya sun rabawa mata marasa karfi kayan abinci .

Tallafin da Kwamishiniyar harkokin Mata da walwala ta jihar Nasarawa Hajiya Halima Ahmad Jabiru ta jagoranci rabawa a makarantar Science School dake garin Lafia.

Da take jawabi Hajiya Halima Ahmad Jabiru ta ce wannan tallafin ya kasance hadin giwa ce da ta hada da tallafin uwargidan Gwamna Hajiya Silifat Abdullah Sule da wata cibiya ta addini dake Abuja da gidauniyya Halima Jabiru gausiyya.

Ta ce halin da ake ciki na wannan watan da kuma matsalolin da ake ciki saboda cutar Korona bairos wanda yanzu haka yake dada yin illa ga rayuwar al’umma.

Ta ce mutani sun shiga halin kunci suna bukatar tallafi mu kuma baza mu zura ido muga jama’a suna rayuwa cikin kunci ba shi yasa komin kasawan shi zamu ba ku.

Kwamishiniyar tayi kira ga matan da suka halarci wannan gurin dasu kula da rayuwan yara qanana. Su riqa tsaftace su , su kuma riqa wanke masu hannaye.

Ta ce matsalar cutar Korona bairos ya addabi ko ina , shi yasa gwamnatin jihar Nasarawa taga ya kamata ta dakile yaduwar cutar ta hanyar takaita zurga zurgan jama’a.

Tace hakan da Gwamnatin tayi ba da nufin takurawa al’umma bane sai domin nuna masu kauna.

Ta bukaci matan da suka halarci wajen karban tallafin da su kasance masu kiyaye dokokin hukumar kiwon Lafiya. Su riqa sanya abin rufe hanci da baki . su kuma daina zama cikin cin koson jama’a.

Ta ce , ko da aka ce a dakatar da Salam jam’i ba an hana sallah bane . a kano Wanda yazo da cutar ya hallarci  sallar jam’i sannan ya hallarci daurin aure, ga shi yanzu Annobar cutar tana illa so sai a kano .

Ta bukaci mutani suyi sallah a gidajensu sannan su cigaba da yin adu’a saboda babu abinda ya gagari Allah.

Tallafin abincin ya hada da shinkafa da indomi da masara da kuma man-gyada.

Wadanda suka amfana da wannan tallafin sun nuna godiyansu ga kwamishiniyar da uwargidan Gwamna da suka taimaka masu da wannan abincin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *