GWAMNONI SUN KULLA YAR JEJENIYAR ZAMAN LAFIYA KAN IYAKAR NASARAWA DA BENUE

GWAMNONI SUN KULLA YAR JEJENIYAR ZAMAN LAFIYA KAN IYAKAR NASARAWA DA BENUE

Daga Zubairu Lawal

A Yau ne  Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa da takwararsa Gwamnan Samuel Oton na jihar Benue suka sanya hannu akan takardan kulla  yar jejeniyar zaman lafiya mai durewa a tsakanin kan iyakokin jihar Nasarawa da jihar Benue.

Taron da ya samu halartan duk bangaren jihohin guda biyu Gwamnonin jihohin da mataimakansu da  ywn majalisar dokoki da Shugabannin kananan hukumomi da sarakuna gargajiya da masu fada aj.

An gudanar da tarone a garin Yalwata wanda nane kan iyakokin jihohin biyu . An gudanar da tarone bisa ga matsalar kan iyaka da yakici yaki cinyewa.

An dade an samu takun saka a wannan kan iyakan wanda ko ina ke ganin shi yake da hakin  mallakar wannan gurin.  Matsalar da ya dade yakan janyo asarar rayuka masamman  tsakanin manoma yan kabilar TV da Fulani makiyaya.

Da yake jawabi Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule yayi kira ga dukkanin bangarorin biyu da su kai zuciya nesa , kuma a gudanar da tattaunawa domin samun maslaha tsakanin alumman jihar Nasarawa da yan jihar Benue da ke rayuwa a wannan gurin.

Ya qara da cewa zub da jini da akeyi tsakanin mazauna kan iyakar baya haifar da natija face asara.

Gwamna Abdullah Sule yayi kira ga Shugabanni Fulani da su gargadi Makiyaya da su kawar da jikinsu daga wannan guri har sai an samu kyakyawar matsaya kan mallakar gurin.

Ya ce kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin Mataimaka Gwamnonin biyu yana da tabbacin za a samar da maslaha a tsakani.

Injiniya Abdullah Sule ya ce  Fulani makiyaya su daina shiga yankin jihar Benue domin kiwo saboda jihar Benue tana da dokar hana yawace -yawace gurin kiwo.

Ya ce , idan suka gudanar da kiwo a yankin Benue sun sabawa doka kuma za a kamasu. Saboda haka su gudanar da kiwon su cikin iyakokin jihar Nasarawa.

Gwamna Abdullah Sule ya qara da cewa ya kira wannan zaman tattauna wa ne domin kaucewa zubar da jini da akeyi a wannan kan iyakar.

Shima a nasa jawabin Gwamnan jihar Benue Mista Samuel Oton ya ce zai yi amfani da jami’an tsaro wajen dakatar da yan kabilar TV dake kwace shanun Fulani a wannan kan iyakar.

Ya bukaci jami’an tsaro dasu kasance masu kulawa kada su bari wani ya cizarafin makiyaya da suke rayuwa a wannan kan iyakan.

Sannan Gwamnan jihar Benue ya bukaci Fulani makiyaya dasu bi tsari wajen shiga jihar Benue domin gudanar da kiwo .

Ya ce , tsarin da Gwamnat

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *