GWAMNA ABDULLAHI SULE NA JIHAR NASARAWA ZAI TAIMAKAWA WADANDA AMBALIYAN RUWA YA RUTSA DA SU A GARIN ARA – MALAM YAKUBU LAMAI

Gwamnar Jihar Nasarawa zaiba da tallafin ambaliyar ruwa.

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Mai girma Gwamnar jihar Nasarawa Injiya Abdullahi A. Sule ya yi wani rangadi zuwa unguwar Ara dake cikin qaramar hukumar Nasarawa  domin ganin ma idon shi irin barnar da ruwan sama ya yi a yan kin  unguwar ta Ara,

Ruwan sama kwmar da bakin kwarya wanda ya yi sanadiyar kar ye wata gada  ta unguwar Sarkin Ara,

wanda kuma sakamakon hakan ruwan ya yi barna so sai a unguwar a inda aka yi asarar kaddarori na dukiya mai yawa. kuma aka rasa wannan gada mai mahimmanci da take kai muta ne zuwa wannan unguwa ta Ara.

Bayan zagayen da Gwamnan Abdullah Sule yayi ya gane wa idanun shi yadda alumman wannan yan kin suka shiga cikin kunci sakamakon wannan ambaliyan ruwan sama da ya zai zaiye wasu gurare bayan kar yewar gadan.

Cikin takardan da mai taimakawa Gwamnan Abdullah Sule ta vangaren manema labarai Malam Yakubu Lamai ya raba

Bayan karbar sakamakon rahotan wannan ambaliyan  ya ce mai girma Gwamna ya kafa wani Kwamati wanda zai rage radadin wannan asara da aka yi, a karkashi jagorancin mai martaba  Sarkin Nasarawa Alhaji Jibril Usman hade da hadin gwiwar Sarkin Ara, da kuma Oche Agatu.

Gwamna Abdullahi  Sulen dai ya yi hakan ne domin taimakon wadan nan mutane da wannan ambaliya ta rutsa da su a wannan Unguwa ta Ara.

Da kayayakin masa rufi na gaggawa da kuma gyaran guraren da ruwan yayi barna domin yanzu lokaci ne  na damuna ta yadda za a samu hanyar shiga da fice ga alumman yan kin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *