GWAMNATOCIN AFIRKA SU BA DA HIMMA WAJEN DA KILE CUTAR COVID-19- Sakataren MDD

GWAMNATOCIN AFIRKA SU BA DA HIMMA WAJEN DA KILE CUTAR COVID-19

Sakataren MDD

Daga Zubairu LAWAL

Majalisar dinkin Duniya ta yi gargadi akan yadda Annobar cutar korona bairus ke yaduwa a Afurika.
Majalisar Dinkin Duniyar ta koka da yadda cutar take ci kamar  wutar daji a Afurka.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mista  Antonio Guterres ya kara da cewa duk da cewa cutar tana kama mutane ba yadda aka zata ba, amma dai abun na da ban tsoro ganin irin yadda cutar ke yaduwa cikin al’umma.

Yayi kira ga Gwamnatocin Nahiyar yan kin Afirka da su zage dantse wajen kokarin dakile yaduwar cutar saboda idan yayi muni to jami’an Nahiyar Afirka zasu shiga mafi munin matsala.

Ya ce , matsalar yan kin Afirka akwai matsalolin tattalin arziki dana kwararun likitoci da rashin ingancin Asibitoci.

Saboda haka su kula da yana yin shiga da ficen mutanin dake shigowa nahiyoyin su. Su kuma dauki matakin dakile yaduwar cutar ta hanyar killace jama’a.

Ya ce dole al’umma zasuyi hakuri na ganin sauyin rayuwa saboda zasu ga kamar ana takura masu.

Wannan matsalar ta Annobar cutar korona bairos dole a dauki irin wannan matakin saboda idan cutar ta shiga cikin marasa galihu to zai yadu tamkar wutan daji, masamman ga alumman karkara.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mista Annobar Guterres ya ce , yanzu haka akalla sama da mutum miliyon daya suka kamu da wannan cutar ta Korona bairos a Nahiyar Afirka.

Sannan sama da mutum 2,500 suka rigayemu gidan gaskiya sakamakon wannan Annobar cutar korona bairos.

Ya yabawa kungiyar tarayyar Afirka wajen zagewa da ba da himma wajen yaki da yaduwar cutar a ciki da waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *