GWAMNATIN NIJERIYA ZA TA KAWAR DA CUTAR COVID-19 A CIKIN KASAN TA

Gwamnatin Nijeriya za ta yi ban kwana da cutar Korona bairos

Inji Aregbesola

Daga Zubairu Lawal

Ministan harkokin cikin gida Mista Rauf Aregbesola ya ce Gwamnatin Nijeriya ta kudduri aniyar kawar da cutar Korona bairos a qasar ba ki daya. Ministan ya bayyana haka sa ilin da tawagar Gwamnatin Nijeriya ke karban kayan agaji da taimakon Kwararun Likitoci da Majalisar Dinkin Duniya ta twimaka da su domin yaki da cutar Korona bairos.

Ministan harkokin cikin gidan ya qara da cewa, Gwamnatin tarayya ta shirya kayan magani domin rabawa dan yaki da cutar Kwaronabairus.

Kayayyakin dai za’a raba su ne a karkashin jagorancin Ministan Cikin gida, Mista Rauf Aregbesola,da Ministan harkokin waje, Mista Geoffrey Onyeama,  sai kuma shugaba mai kula da jindadin Jama’a da taimakamawa idan wani Iftala’i ya faru, Malama Sadiya Umar Faruk.

Tare da tawagar yaki da cutar Korona bairos a Nijeriya da suka halarci wajen gani da ido lokacin da kayayakin suka iso. Ministan ya ce idanuwa sun sheda kuma za a yi aiki da kayyakin yadda ya kamata.

Da yake jawabi a madadin vangaren Majalisar Xinkin Duniya Babban jami’i a fannin yada labarai da sauran ayyuka na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya Mista  Edward Kallon.

Ya ce , wannan tallafine kashi na farko da Majalisar Xinkin Duniya ta taimakawa alumman Nijeriya saboda yadda cutar Korona bairos ke kara bazuwa kuma yana barazanar ga rayuwar alumman qasar.

Ya qara da cewa cikin qasashen da suke fama da yaduwar cutar Korona bairos Majalisar tana mai da hankali wajen ba da taimakon dakile cutar.

Ya ce  wannan kayayakin da aka kawo zai kai na dalan Amurka miliyon biyu. Sannan wannan shine taimakon kashi na farko .

Yayi kira ga Gwamnatin Nijeriya data zage dantse wajen yaki da wannan Annobar cutar Korona bairos dake yaduwa cikin hanzari ga jama’a.

Ya ce Majalisar Dinkin Duniya zata hada hannu da dukkanin qasashen duniya wajen ganin an kawar da cutar Korona bairos wanda ya addabi duniya ya karya tattalin arziki da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *