KO NA SUKA A KUJERAR GWAMNA EFCC BA ZATA ZARGE NI DA SATAN DUKIYAR JIHAR NASARAWA BA

KO NA SUKA A KUJERAR GWAMNA EFCC BA ZATA ZARGE NI DA SATAN DUKIYAR JIHAR NASARAWA BA

Inji Gwamna A.A SULE

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya bigi kirji yadda ya tabbatar wa alumman jihar cewa ko yau ko gobe duk lokacin da ya sauka a kan kujerar Gwamnan jihar ya yi Imani hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa  wato EFCC ba za su tuhume shi da satan kudin jihar ba saboda shi ya san bai taba sata ba.

Gwamna Abdullah Sule ya ce yayi aiki a gurare dabam dabam kuma har yanzu yana alfahari bai bar baya mara kyau ba. da yanzu an zarge shi ko a turo yan sanda su kama shi.

Ya qara da cewa ko ya bar Gwamnan haka zai yi zaman shi babu Dan sandan da za a turo ya tuhume shi akan satan kudin jihar. Saboda ya san amana aka ba shi, bai kuma zo da mummunar manufa ta satan dukiyar al’umma ba.

Da aka tambaye shi dangane da asusun da tsohuwar Gwamnati ta gadar da kuma ayyukan da tayi  me yake ciki ?

Sai ya ce ku tambayi wadanda sukayi aiki da tsohuwar Gwamnati saboda shi ba a yi gwamnatin baya tare da shi ba.

Gwamnan yace ko da ake cewa da shi zai yi karo daya ne a kan karagar mulki shekara hudu. Shi bai dame shi ba saboda ko yau ya sauka ya godewa Allah bai danne hakin kowa ba.

Kuma da ake batun maganar kudin fansho da gara-tuti idan akace za a biya wannan kudin ya kai biliyon arba’in. Ta ina zai samu wannan kudin?.

ya qara bayyana cewa jama’a su fahinci tsarin Gwamnatin sa ba wai fada da karatun allo sukeyi  ko kushe harkan al-majiran ciba.

Gwamnan ya ce  tsarin da suka fito dashi dangane da batun al-majiran ci zai taimakawa al’umma ne.

Gwamna Abdullah Sule ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da zagayowar bikin murnar cika shekaru guda bisa karagar mulki.

Gwamnan yace har ga Allah yadda ake gudanar da tsarin al-majiran ci akwai sake saboda zaka ga yaro qarami wanda shekarun sa ba su kai da ya iya taimakawa kan sa ta wajen ko mai ba, amma za kaga iyayen shi sun turashi wani jihar yana barace barace akan titi da sunan yazo karatun allo.

Malamin al-majirai sunyi masa yawa kuma babu yadda za ayi malamai su iya daukar rayuwar yara qananan dake gaban su.

Ya ce, iyayen yaran nan suna zaune da matansu a gidaje kuma suna kara auratai ya amma suna dauko qananan yara suna turo su wasu jihohin yaran basu samun kulawa suna barace barace.

Ya ce , wannan ne  dalilin da ya sanya Gwamnonin Arewa suka dauki wannan matakin na maida duk yaron qarami gaban iyayen shi saboda ya samu kulawa mai kyau kuma ya fara karatu a can idan shekaru sun zo masa ta yadda zai iya zuwa ko ina niman ilumi ya je.

Gwamna Abdullah Sule ya ce a nan jihar Nasarawa mun tura al-majirai zuwa jihohin kuma cikin kyakyawar kulawa da jin dadi.

Ya kara da cewa a wannan lokacin da ake fama da matsalar cutar Korona bairos an samu matsalar tattalin arziki shi ya sanya abubuwa suka rika tsayawa ba kamar yadda muka tsara ba.

Yace Babban burinmu hanyoyin kudaden shiga muke bukatar kara kirkirowa ta hanyar hakar ma’adinan qar qashin kasa. Saboda samar da wannan ma’adinan zai samar da hanyoyin kasuwanci mai yawa.

Masamman farin ruwa guri ne da zamu samu amfani da yawa. Kuma zamu samu qarfin makamashin wutan lantarki wanda zai bunqasa manya da kananan masana’antu wanda Al’umman jihar Nasarawa zasu samu ayyukan yi na dogaro da kai.

Gwamnan ya kara da cewa Gwamnatin sa tana daraja kowata kabila a jihar Nasarawa kuma tana tafiya da kowa da kowa domin cigaban jihar Nasarawa.

Ya ce , duk kowa Dan jihar ne kowa yana da gudumawar da zai bada domin cigaban jihar Nasarawa. Al’umman jihar Nasarawa masu kaunar junan su ne .

Gwamna Abdullah Sule ya ce fatanshi alumman jihar Nasarawa su samu dauwa mammen zaman lafiya da cigaba mai amfani .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *