KARYA SU KEYI BABU MAI CUTAR COVID-19 A JIHAR KOGI – GWAMNA BELLO
Gwamnatin Jihar Kogi ta karyata hukumar NCDC da ta sanar da cewa an samu mutum biyu masu dauke da cutar korona a karon farko a Jihar.
Kwamishinan lafiya na Jihar, Dakta Saka Haruna Audu ne ya karyata hukumar NCDC din a madadin gwamna Yahaya Bello a wata takardar sanarwar manema labarai da ya sake a ranar Laraba, inda ya ce, zancen nasu karya ne.
Ya ce: “Jihar Kogi har zuwa yanzu ba ta da mai dauke da cutar Korona. Mun samar da tsarin yin gwaji sosai, wanda kuma an yi gwaje-gwajen amma har yanzu babu wanda ke dauke da wannan cuta.
“Mun sanar tun da dadewa cewa babu wanda zai sa mu yi karya wurin ayyana cutar Korona a jihar Kogi alhali babu mai ita.
“Sannan kuma babu wanda ya isa ya tursasa mana sanar da kamuwa da cutar alhali karya ne. Ba za mu lamunta ba.” inji shi