GWAMNATIN NIJERIYA NA BUKATAR KAYAN AGAJIN YAKI DA CUTAR KORONA BAIRUS

Gwamnatin Nijeriya na bukatar kayan agajin yaki da Korona bairos
Inji Dakta Chikwe Ihekweazu.
Daga Zubairu M Lawal

Dakata  Chikwe Ihekweazu shi ne babban jam’in kiwon Lafiya kuma cikin ma’aikatan hukumar yaki da annobar cutar Korona bairos a Nijeriya. Ya ce Gwamnatin Najeriya sanda aka ba da rahoton bullar cutan na farko a ranar 27 ga watan Fabreru, 2020, suna da wajen gajin cutar guda biyar ne kawai a jihohi Hudu cikin qasar baki daya.

Amm da cutar ta cigaba da yaduwa sai hukumar NCDC suka kara wasu abun gwajin suka zama 17, kuma yanzu haka ma suna ta kokarin samar da kayayyakin gwajin ga duk fadin jihohin Najeriya guda 36 domin dakile yaduwar cutat.

Babban jami’in Hukumar yaki da yaduwar Annobar cutar Korona bairos wato NCDC ya ce nan da wata uku muke bukatar samar da wadannan Na’urorin a duk kan jihohin saboda zai taimakawa Ma’aikatan mu a wajen dakile yaduwar cutar.

Ya qara da cewa cikin lokaci qan qani za a iya gwajin kimanin sama da mutum miliyon biyu a cikin qasar. Ya ce kowata jihar zata iya gwaji ga mutani sama da dubu hamsi.

Ya ce wahalar cutar Korona bairos shi ne a gano masu dauke da kwayar cutar. Za a san yadda za ayi masu magani da har za a ci illar Annobar.

Amma idan aka ce an kasa gano adadin masu dauke da kwayar cutar to akwai babban aiki. Saboda duk kokarin da likitoci suke yi ba za a gani ba .

Domin masu dauke da kwayar cutar wadanda ba ayi masu gwaji ba zasu rika yadawa cikin al’umma ta wajen yin mu’amala da su.

Dakata  Chikwe Ihekweazu ya ce dole Gwamnatocin na hiyar Afirka su miqe tsaye saboda babban kalubale yana gaban su. Domin alumman Nahiyar Afirka basu iya kai kansu Asibitochi ana yi masu gwajin kwayar cutar.

Ya ce anyi ta gargadi jama’a su riqa zuwa gwajin kwayoyin cututtuka a Asibitochi amma jama’a basu yarda. Shi ya sanya kullum ake samu karuwan cutar Shuga cutar Qoda, Cutar Hawan jini, ciwon zuciya, cutar HIV da sauran su.

Ya ce ya wajaba Gwamnatoci su dukufa wajen wayar da kan al’umma su fahinci mahimmancin zuwa gwajin kwayoyin cututtuka saboda yakan rage yawan masu cutar.

Duk wanda aka gano yana da cutar magani za a yi masa ya warke. Idan ya warke ba zai iya yada ta zuwa ga wani ba.

Dakta Chikwe Ihekweazu ya ce yanzu kullun cutar Korona bairos ya duwa takeyi  masamman a qasar mu Nijeriya duk da kokarin da Gwamnati da Malaman kiwon Lafiya ke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *