ILUMI A LOKACIN KORONA M.D.D TA YABAWA YAR NIJERIYA DAKE KOYAR DÀ YARÀ KARATU A GIDA

Ilumi a lokacin Korona Mdd ta yabawa yar Nijeriya dake koyar da yara a gida

Daga Zubairu M Lawal

Cutar Corvid-19. Majalisar dinkin Duniya ta bukaci a cigaba da koyar da ilimi daga gida.
Malisar ta yabama wata malama yar Nijeriya mai suna Malama  Rosina Amos,  wace take aiki da kungiyar kula da qananan yara na Majalisar Xinkin Duniya UNICEF. Majalisar ta yaba mata ne saboda matakin da ta dauka wa kanta  na   koyar da yara karatu a cikin Al’umman daga gidajen su, dake kauyen   Dampo cikin jihar Borno.

Da yake yabawa da wannan kokarin na Malama Rosina Babban jami’i a ofisin kula da qananan yara ta Majalisar Xinkin Duniya Mista  Olayinka Adeseja ya ce , majalisar ta ce wannan sabon cigaba ne, kuma abun a yaba ne,  kuma ya kamata sauran mutane suyi koyi da ita.

Ya qara da cewa sanin mahimmancin ilumin yara ya sanya Malama Rosina ta dukufa wajen ganin yaran dake tasowa daga yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, sun samu ilumi mai inganci kada su koma gidan jiya.

Saboda zaman su a gida zan zanya su shagala da rashin samun ilumi kamar yadda suka ka sance a baya lokacin da yan ta’adda suka rika koran al’umma daga gidajen su.

Ya ce Malama Rosina ta du kufa wajen koyar da yara fannin turanci da lisafi.

Ya ce Annobar cutar Korona bairos ta sanya miliyoyin yara suna zaune a gidajen su sakamakon rufe makarantu da Majalisar Xinkin Duniya ta sanar domin dakile yaduwar cutar Korona bairos.

Kuma aka shawarci malamai su riqa koyar da yara karatu a gidajen su.

Ya ce , wannan gudumawa da malama Rosina ta bayara ga alumman karkara su . abune da ya dace ace mutani da dama sun dauki wannan tsarin zai taimakawa yara qanana dake zaman gida.

Ya ce Malama Rosina ta nuna kishi saboda a baya yaran yankin Arewa maso gabashin Nijeriya sun sha bakar wahala . yanzu sun fara farfaduwa bata bukatar taga karatun su ya tsaya.

Saboda da damansu sun kasance cikin rayuwa a sansanin yan gudun hijira ba tare da kwakwarar kulawa ba. Bare karatu mai inganci da zai daga darajar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *