YADDA MAGA TAKARDAN KWALAJIN HORAR DA MALAMAI YA KASHE MILIYOYIN KUDI BA BISA KA’IDA BA A KATSINA

YADDA MAGA TAKARDAN KWALAJIN HORAR DA MALAMAI YA KASHE MILIYOYIN KUDI BA BISA KA’IDA BA A KATSINA

Maga takardan Kwalejin Horas da Mallamai na Gwamnatin Tarayya dake Katsina Garba Isyaku Dan tuture ya tabbatar da yayi amfani da sama da naira miliyan arba’in ta hannun Jami’i Mai Kula da Kude na Makarantar wato bursar domin samun nasara a kotu bisa korarsa da akayi.

Magatakar dan Kwalejin, Garba Isyaku ya bayyana haka ne a hiransu da suka yi ta wayar tangaraho kuma aka yadda a kafaffen sadarwa na zamani.

Ya kuma tabbatar da yayi amfani da offishin sa ya dauki aiki ba akan ka’ida ba sai dai saboda sanayya ga iyayyen yara dama wasu mutum ashirin da ya dauka a jihar Gombe.

Ga wasu muhimmman bayanai wadda aka fitar dasu daga firar na su.

HARSASHIN SABBIN KASHE KASHE A KARAMAR HUKUMAR KAFOR TA JIHAR KATSINA.

Sabon rikicin siyasa da ta’addanci ya kunno kai a Karamar Hukumar Kafur da ke Jihar Katsina, Hakan ya bayyana ne a cikin bayanin a wasu faya-fayen munanan maganganu da Hukumomin Tsaron Jihar Katsina suka samu a inda Magatakar dan Babbar Kwalejin Ilimi Gwamnatin Tarraya (FCE) da ke Katsina Garba Isiyaku Dantuture ya yi.

Ga wasu daga cikin ikirarin batanci da tanajin fitina wanda Garba Isiyaku Dantuture ya yi:

1, Shirya taro a asirce ba tare da izinin hukuma ba, kuma a lokacin da Gwamnatocin Tarraya da na Katsina suka hana tarurruka.

2, Halartar taro da makamai don tallafawa kansa.

3, Yin rantsuwa da shan alwashin sai ya haddasa rikicin da za’a kashe fiye da mutane 100 domin cimma burin kashin kansa.

4, Horas da ‘yan ta’adda da saya masu muggan haramtattun makamai da ba su umurnin su kashe duk wadanda ba su yarda da ra’ayi irin nasa ba.

5, Bugun kirjin zai yi amfani da jahilcin al’ummarsa domin tada babban fitina da zai janyo kashe kashen mutane a Yankin Daneji, a inda nan ne mahaifarsa.

6, Yin taro da matasan garin Dankanjiba da ba da umurnin a kashe Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Kafur Hon. Garba Hussaini Dankanjiba, wanda shi haifaffen garin ne.

7, Ba da umurnin a kashe Alhaji Bello Kagara wani babban mai fada, aji aminin Mai Girma Gwamna Jihar Katsina kuma Darakta a Gwamnatin Tarraya.

8, Daukar alkawarin kallubalantar da Gwamna Aminu Bello Masari da kawar das hi mudin ya neme ya tsare masa gaba.

9, Daura damarar korar duk ‘yan siyasar da ke yankinsa da Karamar Hukumar Kafur.

10, Fitowa karara ya ce baya kaunar duk wani dan siyasa da ke Karamar Hukumar Kafur’, Wanda hakan ya sanya ba ya hurda da ko daya daga cikinsu.

11, Yin amfani da offishinsa domin dauka da horas da ‘yan ta’a’ddanci a fakaice a Yankin Daneji.

12, Daukar nauyin kai ziyarar mako -mako a yankin Daneji domin horas da matasa yan juyin juya hali.

13, Yin miyagun maganganu da tsinuwa ga dukkan manyan Karamar Hukumar Kafur da nada kansa sabon jagoran juyin juya hali a wannan karamar hukumar.

14, Sayawa da horas da matasa fiye da dari biyu a tashin farko tabar wi-wi da kaisu filin taro domin aikin ta’adanci.

15, Kama sunan Mai Girma Sanata Muhammadu Danjuma Goje, Tsohon Gwamnan Jihar Gombe karara a matsayin wanda ya horas da shi wajen ta’a’dancin da kisan bayin Allah.

Kafin aji ta’asar da mugun shirin Garba Isyaku Dantuture sai dai ya zama wajibi, kuma hakki ne akanmu mu yi kira ga jama’a a matakin Karamar Hukumar, da Jihar Katsina dana Tarayya su dauki babban mataki a kan wannan batu, musamman idan aka yi la’akari da irin mawuyacin halin tsaro da Jihar Katsina take ciki.

Kada ayi shirin ta leko ta koma yayin da Jihar Katsina ta hango sauki ta hanyar daukin da Gwamnatin Tarayya ta kai mata, akwai tashin hankali a samu shirin aikin aika aika don kurum cimma burinsa.

Bayan wannan , akwai bukatar tsauraran matakai don kare rayuwar mutanen wannan Karamar Hukumar daga sharrin wannan masharrancin ma’aikaci.

Babbar maganar itace, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, a karkashin Ministan Ilimi, Mal. Adamu Adamu da hukumar FCE Katsina da su saurari kalaman Magatakarda Garba Dantuture domin nazarin hadarin da ke tattare da zamansa a tsakiyar dalibai yara a babbar makaranta irin wannan inda ake horar da dalibai kuma malamai.

Don haka muna kira da a dubi hanyoyin da ya bi ya zakulu yaran da yake ikirarin ya dauka aiki. Shin an bi ka’idojin daukar aiki? Koko kamar yadda yake ikirari shi kadai ke da ikon daukar ma’aikata a wannan makaranta.

Muna kuma kira da babbar murya a dauki wadannan matakai don kare wannan makaranta, Jihar Katsina da ma kasa Nigeria baki daya.

Ya kamata hukumar EFCC ta binciki kalamunsa na barnar kudi sama da naira miliyan 40 a makaranta irin wannan a lokacin shari’ar korarsa da aka yi.

Kira na karshe shi ne, kungiyoyin Wayarda Kan Jama’a masu zaman kansu CSO su tashi tsaye don ganin an kare al’ummar wannan Karamar Hukumar da wannan makaranta daga sharrin wannan danta’a’dda.

Bincikenmu ya nuna cewa tarihi ne yake maimaita kansa domin hukumar wannan makaranta ta taba korarsa bisa laifuffuka masu kama da wadannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *