YANZU YANZU MAJALISAR JIHAR NASARAWA TA UMMURCE GWAMNA ABDULLAHI SULE YA KORE SAKATAREN GWAMNATI ALIYU TIJJANI

YANZU YWNZU MAJALISAR JIHAR NASARAWA TA UMMURCE GWAMNA ABDULLAH SULE YA KORE SAKATAREN GWAMNATI ALIYU TIJJANI

Majalisar ta ummurce Gwamnatin ta kore Sakataren ne sakamakon Saminsa da akayi da rub da ciki na miyiyoyin nairorin kwangilar Makarantun jihar lokacin yana matsayin Kwamishinan Ilumi.

Bayan miqa rohotun binciken kwamitin Hon. Daniyel Ogazin dai ya bayyana cewa tsohon kwamishina ba shi da kwarewa wajen gudanar da aikin sa a ofishin sa. A binciken da suka gudanar dai ya nuna cewa tsohon kwamishinan wanda a yanzu haka shi ne SSG, ya hada baki ne da shugabannin malaman makarantun Sakandare da kuma shugabannin ‘yan kwangilar da aka ba aikin wurin wawure wadannan zunzurutun kudaden.

Ya cigaba da cewa adadin kwangilolin da aka bayar, sun kai na Naira 1,084,000,000, amma kuma bincike ya nuna an kashe Naira 873,233,942,60. Amma shi a lisafin tsohon kwamishinan sai ana nuna an kashe 210,766,057,40. Sannan kuma an gano wasu kudi wadanda ba’a saka su a banki ba har Naira 248,484,556,60 da aka yi sama da fadi da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *