JAMA’A SU KULA DA YADDA ZASU KARE KANSU DAGA CUTAR COVID-19 – SAKATAREN MDD

JAMA’A SU KULA DA YADDA ZASU KARE KANSU DAGA CUTAR COVID-19 – SAKATAREN MDD

Daga Zubairu M Lawal

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio Guterres yayi kira ga al’umman Duniya dasu kula da yadda zasu iya dakile kan su daga kariya na Annobar cutar Korona bairos.

Ya ce, cutar Korona bairos zata cigaba da yaduwa na cikin al’umma matukar al’umma suna mu’amala da junan su ba tare da ba da kyakyawar kulawa ba.

Ya ce babu yadda za a yi ace al’umma zasu cigaba da zama a gida ba tare da gudanar da harkokin yau da kullun ba.

Saboda zuwan cutar Korona bairos ya dur kusar da tattalin arziki al’umman Duniya da dama. Harkokin kasuwanci dana aikin Gwamnati dama al’amura sun tsaya cif. Hakan ya sanya jama’a suka shiga cikin wani hali na kuncin rayuwa da muguwar talauci.

Ya ce amma dole a samar da sausauci jama’a su riqa gudanar da al’amurar harkokin su.

Saboda nimawa kai abin tsare gida tare da iyalai.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya qara da cewa wannan Annobar ta cutar Korona bairos ba za ta rabu da jama’a ba. Saboda cuta ce mai zaman kanta sai dai idan jama’a suka dauki mataki to cutar ba za ta riqa ya duwa kamar yadda tayi a baya ba.

Dole a dauki matakin bada tazara tsakanin al’umma da kaucewa guraren cin koson jama’a. Da yawan tsaftace muhali da hannaye. Da sanya takun-kumin rufe hanci a ko yau she.

Ya ce wannan shine hanyoyin da kile ya duwar cutar cikin al’umma. Saboda a halin yanzu akwai miliyoyin mutani da suke dauke da cutar Korona bairos. Wasu suna ganin likita wasu kuma ba suma san suna dauke da cutar ba.

Ys qara da cewa idan ba a bar jama’a ko kuma ba a saki ayyuka da makarantu ba. To karayar tattalin arziki zai karu so sai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *