Arsenal Ta Lashe Kofin Kalubalen Ingila Na FA Bayan Doke Chelsea Daga Ibrahim Lawal

Arsenal Ta Lashe Kofin Kalubalen Ingila Na FA Bayan Doke Chelsea

Daga Ibrahim Lawal

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta doke abokiyar hamayyarta wato Chelsea da ci 2 da 1 a  wasan  karshe da suka fafata a daren jiya a filin wasa na Wembly, wanda hakan ya sanya Arsenal ta lashe kofin gasar FA din na Ingila.

Tun farko dan wasan gaban Chelsea, Christian Pulisic ne ya fara sanya kwallo a ragar Arsenal a minti na biyar, kafin daga bisani Emerick Aubameyang ya farkewa kungiyarsa ta Arsenal a minti na 28.

A minti na 67 kuwa, Aubameyang, ya karawa Arsenal kwallo ta biyu wanda hakan ya bai wa kungiyarsa nasara.

A  yayin karawar Chelsea ta kammala wasan da ‘yan wasa goma, bayan da alkalin wasa ya bai wa dan wasan tsakiyar ta Mateo Kovacic katin kora wato jan kati, sakamakon ketar da ya yiwa dan wasan Arsenal Xhaka.

Nasarar da Arsenal ta yi, ya bata damar shiga cikin jerin Kungiyoyi uku da za su wakilci kasar Ingila a gasar kofin Europa a shekarar badi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *