KUNGIYOYI DABAM DABAM SUN YABA DA AIKIN UWARGIDAN GWAMNAN NASARAWA HAJIYA SILIFAT

KUNGIYOYI DABAM DABAM SUN YABA DA AIKIN UWARGIDAN GWAMNAN NASARAWA HAJIYA SILIFAT

Daga Zubairu Lawal

Kungiyoyin mata daga sasan jihar Nasarawa na kara tururuwa zuwa kai jinjina da wabawa game da ayyukan alheri da uwargidan Gwamnan jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullah Sule take yi.

A baya baya nan Shugabannin kungiyar mata ta kungiyar 4+4 daga yankin karamar hukumar Kokona sun ziyarce Hajiya Silifata Abdullah Sule a gidan ta dake garin gudi dake karamar hukumar Akwanga.

Kungiyoyin suna yabawa Hajiya Silifata Abdullah Sule ne saboda bajintar da gidauniyarta ta SAS take gudanarwa na taimakawa da kuma kare martabar mata da yaki da Fyade da hanna cin zarafa mata a fadin jihar. Sun kuma yi mata fatan alheri da taya ta bukin Sallah babba.

Kungiyoyin sun yaba da rawar da Uwargidan Gwamnan ke takawa na kirkirar hanyoyin taimakawa matan jihar Nasarawa cikin Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *