ZA A TAIMAKAWA MASU CUTAR COVID-19 DA YAN GUDUN HIJIRA A YAN KIN AREWA MASO GABAS

ZA A TAIMAKAWA MASU CUTAR COVID-19 DA YAN GUDUN HIJIRA A YAN KIN AREWA MASO GABAS

Inji Edward  Kallon

Daga Zubairu Lawal

Hukuma mai jinkan Jama’a a Najeriya wato,  FUND a takaice,  sun bayyana cewa za su taimaka ma Al’ummar da annobar Cutar Covid-19 ya tagayyara da kuma wadanda yaki ya dai dai ta su yankin arewa maso gabashin Nijeriya da suka hada  jihohin Borno da Adamawa da Yobe.

Tallafin da za’a baiwa mutanin da suka tsince kansu cikin wannan matsalar rayuwa kuma suna fama da rashin galihu zasu taimaka masu da abubuwan rayuwa da takai na Dalan Amurka Miliyon 22.4.

Babban Kodineto a cibiyar yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya Mista Edward Kallon ya bayyana haka yayi tunawa da halin da yan gudun Hijira suke shiga a lokacin rigin-gimu.

Ya ce , a watar Fabirirun 2017 al’umma sun qara kwararowa zuwa sansanonin yan gudun Hijira dake jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Ya ce yanzu shekaru goma sha daya ke nan da kirkirar sansanonin yan gudun Hijira dake yankin Arewa maso gabas maimakon a samu sauki amma abin ya ci tura kullun lamarin sai qaruwa yakeyi.

Yace Majalisar Dinkin Duniya ta na qara kira ga al’umman Nijeriya masamman masu fada aji dasu taimakawa matasa da ayyukan yi saboda rashin aikin yi wani bangare ne, na kirkirar hanyoyin tashin hankali.

Mista Edward Kallon ya qara da cewa yawan mutanin dake yankin Arewa maso gabas sun ragu so sai sakamakon yadda rigin-gimu suka lalata rayuwar su.

Ya ce dole a tausaya masu saboda yadda yaki ya dai dai ta su, yanzu kuma ga masifar annobar cutar COVID-19 da ya fada cikin sansanonin yan gudun Hijira dake yan kunan.

Hakan ya sanya hukumar jin kai taga ya kamata ta bada karfi a yankin Arewa maso gabas inda suke fama da matsalar rayuwa fiye da ko’ina.

Kimanin mutanin kauyuka da dama a yankin Arewa maso gabas sun rayua ne a sansanin yan gudun Hijira, inda sai an kawo an basu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *