IKON ALLAH – CUTAR COVID-19 YA YI SANADIYAR RUFE MAKARANTU KIMANIN MILIYON 250 A DUNIYA

CUTAR COVID-19 YA YI SANADIYAR RUFE MAKARANTU KIMANIN MILIYON 250 A DUNIYA

Daga Zubairu M Lawal

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio  Guterres ya ce annobar cutar Korona bairus ya lalata harkan ilumi da aka dauki tsawan shekaru mai yawa ana ba dawa.

Ya ce yanzu haka kimanin makarantu miliyon 250 ne suke rufe sakamakon yaduwar annobar cutar Korona bairus. Sannan akwai dalubal kusan biliyon daya dake zaman gida.

Wajibi ne a samar da hanyoyin magance yaduwar cutar Korona bairus a Duniya.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio Guterres ya fadi haka ne a birnin New York ta kasar Amurka wajen taron lalubu hanyoyi ko mafi akan ilumin yara.

Ya ce a tsakan kanin watan yuni zuwa yanzu sama da kasa shen Duniya 160 suka rufe makarantu. Inda sama da yara biliyon daya  suka komai zaman gida.

Ya kara da cewa wajibi ne mu samar da hanyoyin da zamu koma makarantu domin baiwa dalubai ilumi. Amma asan hanyoyi masu inganci da zai kare yara daga kamuwa da cutar Korona bairus.

Duk idan za’a koyar da karatu wajibi ne a tanadi kayayakin da suka hada da takunkumin San yawa a fuska da sabulan wanke hannaye da man shafawa a hannaye lokaci bayan lokaci.

Ba za a rabu da cutar Korona bairus cikin sauki ba kuma baza mu zura ido mubar yara suna zaman gida babu harkan ilumi ba.

Ya ce akwai hanyoyi da yawa na koyar da karatu amma ba ko ina bane hakan zai iya amfani.

Ana iya koyon karatu ta gidan talabijin ko gidan radio da sauransu amma da dama ba zasu iya ba.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu dalubai kalilan ne ke iya karatu ta hanyoyin sadarwa .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *