AN DAKATAR DA MAI UNGUWAR DA AKE ZARGI DA SAYAR DA JARIRI A JIHAR KANO

AN DAKATAR DA MAI UNGUWAR DA AKE ZARGI DA SAYAR DA JARIRI A JIHAR KANO

Daga wakilinmu

Masarautar Kano ta dakatar da mai unguwar Sabon Gari mallam Ya’u Muhammad, bayan da aka zarge shi da hannu a sayar da wani yaro mai shekara daya.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da masarautar ta Kano ta fitar a daren Talata daga ofishin Galadiman Kano kuma babban dan Majalisar sarkin na Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

Ana dai zagin mai unguwar Malam Ya’u tare da shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar Fagge Jamilu Yusuf da sayar da wani jariri ga wata mata kan kudi naira dubu 20.

Mataimakin sakataren masarautar Awaisu Abbas Sanusi, ya shaida wa manema labarai cewa, an dakatar da mai unguwa Ya’u ne bayan rahoton da hakimin Fagge Alhaji Mamuda Ado Bayero ya gabatar a gaban sarki Kano.

An dai dakatar da mai unguwar ne har sai hukumomi sun kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *