MACE MUSULMA DA TA FARA HURA WASAN KWALLON KAFA TA FARKO A KASAR BIRTANIYA

MACE MUSULMA DA TA FARA HURA WASAN KWALLON KAFA TA FARKO A KASAR BIRTANIYA

Daga Ibrahim Lawal

“Mutane ba sa iya fadin alheri, amma hakan ba ya rage min kwarin gwiwa.”

Mace Musulma lafari ta farko a Birtaniya ta ce burinta shi ne ta busa wasa a mataki mafi girma a Birtaniya, kuma ta karfafa wa mata da yawa gwiwar bin sahunta.

Jawahir Roble tana shekara 10 a duniya lokacin da iyayenta suka yi gudun hijira zuwa London bayan tserewa yakin basasa da ake yi a Somaliya.

Zaman da ta yi karkashin inuwar filin wasa na Wembley da kuma kwallon kafar da ta buga a firamare su ne matakin farko da ya sanya mata burin zama lafari.

A wata tattauna wa da ta yi da BBC, Jawahir mai shekarar 25 ta bayyana yadda ta koyi turanci da kuma yadda ta yi fama da nuna wariya da kuma cimma burinta.
‘Na so na buga wa Ingila tamaula’
“Na so na buga wa Ingila wasa,” in ji ta.

An san Jawahir a matsayin ‘JJ’ kuma ba ta iya turanci ba lokacin da suka isa Birtaniya.

Ta tuna yadda ‘yan ajinsu na firamare suke gaza fahimtar turancinta da yadda take fama ta yi magana daidai, amma nan da nan ta shawo kan matsalar saboda son da take yi na koyon harshen.

Ta ce: “Ban iya turanci ba amma kwallon kafa na birge ni tun daga ranar farko. Ina zuwa da kwallona kuma a firamare duk wanda ya je da kwallonsa ne sarki. Duka maza da mata da ni suke wasa abin gwanin dadi.

“A ajin turanci zalla ake yi nakan rudewa idan ana magana, da yara kawai nakan iya magana. Nakan ce ‘ku taimaka ku wurgo min kwallon, na gode, sai na harba’.

Kalmomin haka suke fitowa kai tsaya, irin abin birgewar nan, ina magana da turanci.”

“Na so bugawa Ingila wasa amma iyayena na ganin hakan ba zai taba faruwar ba,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *