SHAHARARIYAR YAR KWALLON KAFAN NIJERIYA TA YAR DA HARKAN KWALLO TA KOMA SANA’AR KITSO

SHAHARARIYAR YAR KWALLON KAFAN NIJERIYA TA YAR DA HARKAN KWALLO TA KOMA SANA’AR KITSO

Daga Ibrahim Lawal

Yayin da kika samu nasarar komawa matsayi mafi girma daga ƙasa – zuwa mataki mafi girma a gasar kwallon kafar ƙasarki a ƙungiyar matan da ta fi samun nasara – dole za ki yi tunanin jin dadi na nan tafe.

Wannan ne halin da Chinenye Okafor ta tsinci kanta a ciki, amma ba haka abin yake ba kwata-kwata.

Okafor, ita ce mataimakiyar kyaftin din ƙungiyar Pelican Stars. Ta hakura da kwallo ne a watan Yuni saboda ƙin biyansu kuɗaɗensu na sama da shekara guda, ta kuma koma aikin kitso da gyaran kai.

“Ba zan iya fada wa kowa cewa ‘yar kwallo ba ce ni saboda kunya nake ji bayan damuwar da nake da ita a kan kwallo na tsawon shekara 22 amma babu abin da na cimma a cikinta,” matashiyar mai shekara 22

“Yanzu ni mai kitso ce da gyaran kai kuma ina ganin ci gaban hakan. Zan iya cigaba da rayuwata. Ina fara aiki daga karfe 8:30 zuwa 5:30 daga Litinin zuwa Asabar. Akwai wuya amma na gode wa Allah domin ina samun kudi.”

Akwai matukar bambanci da lokacin da take ƙoƙarin ganin ta cimma dogon burinta na wasan kwallon ƙafa wanda ta sha matuƙar wuya a kanta, yayin da jami’an ƙungiyar suka gaza biyan tawagar mata haƙƙ oƙinsu.

“Ina yin kuka a wasu lokutan cikin dare saboda idan gari ya waye ba ni da abin da zan ci.

“Bayan karo biyu ko uku, na yanke shawarar na koma Legas – saboda ba zanci gaba da shan bakar wahala ba,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *